Data Offer

Yadda zaka karbi bashin data a layin Airtel cikin sauki a 2022

Bashin data a layin airtel

Yadda zaka karbi bashin data a layin Airtel cikin sauki a 2022

ko kasan zaka iya karban bashin datan Airtel domi ci gaba da bincike a yanan gizo da zaran datan ka ya kare?

Idan kana bukatan neman bashin data a layin Airtel to kana inda ya dace domin wannan rubutun zai a takaice zai taimaka maka, a cikin wannan rubutun, za kuma ka koyi abubuwa da dama wadanda suka shafi data a layin ka na Airtel ba tare da kasha wahala ba.

Sannan zaka koyi yadda zaka checking data balance din ka, har ilau dai a wannan rubutun zaka koyi yadda ake sayan d ata a layin Airtel, da kuma yadda zaka duba balance na datan da ka karba bashi a layin Airtel.

A yanzu da kake karanta wannan rubutu kana neman hanyar karban bashin data ne a layin Airtel, idan kai cikakken mai amfani da yanan gizo ne kamar ni nasan kasan zafin da mutum yake ji a yayin da yake bincike aka internet data ta kare masa.

karanta: https://absanresource.com/2022/05/04/yadda-zaka-karbi-bashin-kudin-kira-a-layin-mtn-borrow-airtime/

Nasan kuma mutane masu dumbin yawa sun san ana iya karban bashin data a layin Airel sannan kuma sun san yadda ake karban bashin kudi a layin a layin Airtel, to a yanzu kuma zan nuna maka yadda ake karban bashin data a layin Airtel cikin sauki.

Mun gode Allah Airtel ma sun samar da tsarin bada bashin data kuma yanzu zan nuna maka yadda za kayi. Bakin cikin da muke shiga a yayin da data ya kare mana musamman a lokacin da muke nesa da masu sayar da kati yazo karshe domin ko a cikin daji muke idan dai da network to kai tsaye zamu nemi bashi domin muci gaba da binciken mu a shafukan yanan gizo.

Ina da tabbacin wannan tsarin da suka fitar na bayar da bashi zai taimakawa mutane masu dumbin yawa wadanda ba lallai ne ma su iya kididdiguwa ba, idan bukatan ka shine koyon karban bashin datan Airtel kana inda zaka koya kuma a kyauta.

Da akwai matukar cin rai, mutum yana kasancewa cikin yanayi maras dadi idan data ya kare masa, kuma mutum yakan fi jin zafin ne a yayin da yake wani abu me muhimmanci datan ta kare masa kamar yadda kaima wata kila ka taba kasancewa cikin irin yanayin.

Matakan karban bashin data a layin Airtel

  • Akan wayar sai ka danna *500#
  • Sai ka zabi 3 domin karban bashin data a layin Airtel
  • Daga nan sai ka zabi yawan datan da kake bukatan karba.

Shikenan an kammala karban bashin data a layin Airtel, bayan kabi wadannan matakai datan zai shigo layin ka. Sai dai fa ba kowa ne yake da daman karba ba saboda akwai sharruda da suke bukata mutum ya cika kafin su bashi bashi, idan baka cika ba baza su baka ba.

Dokoki da sharrudan karban bashin data a layin Airtel

  1. Dole ne layin ka ya kasance yana da register kuma ana kira dashi
  2. Ya kasance kayi amfani da layin ka har na tsawon kwanaki 90.
  3. Kuma layin ya zama ana sa masa kati a kai- a kai.
  4. Ya kasance basa bin ka wani bashi kamar na airtime d.s.

Idan kasan ka cika wadannan dokoki to ba kada matsala kana iya zuwa karban bashin data na layin Airtel.

Wannan shine cikakken rubutu game da yadda zaka karbi bashin datan layin Airtel, idan kana da wata tambaya zaka iya tura mana ita ta comment domin bada amsa idan Allah yasa mun sani kuma kar ka manta kayi sharing wannan rubutu zuwa ga abokan ka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button