Airtime Offer

Yadda zaka karbi bashin kudin kira a layin MTN (Borrow Airtime)

Yadda zaka karbi bashin kudin kira a layin MTN (Borrow Airtime)

Yadda zaka karbi bashin kudin kira a layin MTN (Borrow Airtime); Nasan kana neman yadda ake cin bashi ne a layin MTN.

Kar ka daga hankalin ka, ba kai kadai bane kake neman yadda ake karban bashin kudin kira ba, akwai mutane bila adadin da suke neman bashin kudin kira a layukan sadarwan da suke amfani dasu.

Cikin ikon Allah sai ya kasance kaci karo da rubutu na akan yadda zaka karbi bashin kudin kira a layin MTN domin ka biya daga baya.

A yau zan nuna maka hanyoyi guda uku dodar domin neman bashin airtime da kuma muhimman abubuwa da ya kamata ka sani game da karban bashi a layin MTN.

KARANTA: Yanda zaka bude kuda bank account da wayar ka

Game da karban bashin kudin kira a layin MTN

Wannan tsari na karban bashin kudin kira a layin MTN ana kiran shi da suna MTN Xtratime, duk sanda katin ka ya kare zaka iya dubawa ko kana da daman cin bashi domin ci gaba da kira ko sayan datan hawa yanan gizo kuma ka biya daga baya, bayan ka samu kudi.

MTN suna taimakawa wajen bada bashi domin kira akan lokaci, katin ka zai iya karewa kuma kana bukatan kira cikin gaggawa sannan kuma babu masu sayar da kati kusa da inda kake

To kaga kenan a dai-dai wannan lokaci zaka iya karban bashi nan take zasu baka indai ka cika sharrudan karban bashin sai ka biya su daga baya, wannan taimako ne.

Ta yiwu ma kila cikin tsakiyan dare ne ko kana jeji ko kan hanya yayin tafiya ko kuma kana gurin da ba a samun katin sayarwa kuma gashi katin ka ya kare kuma kiran ujila ya kama ka.

Me yakamata kayi a wannan lokacin? Kawai lambobin karban bashin zaka danna sai ka karba kaci gaba da wayan ka kafin ka isa inda ake samun kati ka say aka biya MTN bashin su da ka karba.

Muhimman abubuwan da ya kamata ka sani game da karban bashi a layin MTN.

Kafin ka yanke hukuncin karban bashin airtime a layin MTN akwai abubuwan da ya kamata ka sani:

 • Ka tabbatar kana da layin MTN wanda yake tafiya
 • Sannan kuma dole ne layin ya kasance da register
 • Ya kasance layin ya kai wata sha biyu ana amfani dashi sannan ya kasance an sa kati kamar na wata uku a jere, ta nan ne zaka iya kasancewa cikin masu daman samun bashin kudi a layin MTN
 • Zasu cire kasha 10 na kudin daka karbi bashi
 • Nan take zasu cire kudin da suka baka bashi da zaran kasa kati a layin

Idan ka cika sharrudan shikenan kawai sai ka antaya domin karban bashin ka.

Yadda zaka karbi bashin kudin kira a layin MTN (Borrow Airtime)

1. yadda zaka karbi bashin kudi a layin MTN

 • Ka danna *606*, za kaga abubuwa da dama sun baiyana akan fuskan wayar ka
 • Ka shiga Xtratime
 • Ka zabi yawan kudin da kake bukatan karba

Nan taka zaka samu sako daga MTN na kudin da ka bukata

2. yadda zaka karbi bashi da *123#

 • Ka danna wadannan lambobin *123#
 • Ka zabi ‘6’
 • Ka zabi Xtratime daga cikin options da zai baka
 • Zabi kudin da kake bukata
 • Ka karbi sakon da MTN suka turo maka (confirmation message)

Nan take zasu turo maka kudin ba tare da bata lokaci ba.

3. karban bashi ta hanyar kira

 • Ka kira wannan lamba 606, kamar dai yadda ka saba kiran lamban waya.
 • Bayan sun dauka zasu baka daman zaban yare sai ka zaba
 • Daga nan zasu baiyana maka kasha-kashen bashin da zasu iya bayarwa sai ka kasa kunne da kyau ka saurara ka zabi wanda kake bukata.

Bayan kun kammala,  bada dadewa ba MTN zasu turo maka sakon katin da ka bukata.

Wannan sune hanyoyin karban bashi a layin MTN, kuma kowa zai iya samun bashin matukar ya cika ka’idodin da muka baiyana a sama.

Wannan rubutun ya amfane ka?

Turawa abokan ka domin ta yiwu daga cikin su akwai masu bukatan sanin yadda ake karban bashin kudin kira a layin MTN, taimaka musu ta hanyar tura musu link na wannan rubutu ta watsapp, facebook, ko twitter.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button