Data Offer

Yadda zaka sayi 1.5GB akan Naira 300 a layin MTN (MTN Data Promo)

Yadda zaka sayi 1.5GB akan Naira 300 a layin MTN (MTN Data Promo)

Shin ko kana neman yadda yadda ake sayan datan 1.5GB akan Naira 300 a layin MTN? toh wannan rubutun  naka ne domin kai a kayi

Sayan data a layin MTN ta sananniyar hanya ba shine damuwan ba. Eyh kawai zaka iya latsa wadannan lambobi kamar haka *131# akan wayar ka kuma ka sayi data irin kalan da kake bukata.

Matsalan shine bin wancan hanyar yana jawo kasha kudi mai yawa, a yanzu haka idan ma baka sani bane to MTN tana bada wani garabasa wanda take bada 2GB akan Naira 500, IGB akan Naira 200, har 1.5GB ma ana iya samu akan Naira 200 da dai sauran su.

karanta yanda ake karban bashin airtime a layin MTN: https://absanresource.com/2022/05/04/yadda-zaka-karbi-bashin-kudin-kira-a-layin-mtn-borrow-airtime/

Abunda ya kamata ka sani game da 1.5GB akan #300

Abun farin cike ne ace duk me amfani da layin MTN zai iya samun data mai sauki akan Naira 300 kacal. Kawai kasa katin Naira 300 sai ka samu data har 1.5GB kai wannan dadin ya kai inda ya kai.

Kuma da wannan datan zaka iya amfani dashia waya, table, computer kai a takaice dai ko wace irin device kake amfani dashi wannan datan zai maka aiki kuma ako wace irin browser.

Wannan tsarin na 1.5GB data bai dade sosai da fitowa kuma a yanzu haka mutane da dama masu amfani da layin MTN suna cin moriyar sa domin a yanzu dai kam zai yi wahala a samu wani tsarin sayan data a layin MTN da yakai wannan sauki.

Kuma abunda nake so ka sani shine wannan tsarin nima da nake rubutu akai nayi amfani dashi kuma ina kan amfani dashi kuma har a yanzu da nake rubutun dashi nake amfani kuma nasan mutane da dama wadanda suma suke cin moriyan tsarin.

Yanzu kai ma ya dace ka shiga wannan tsarin domin samun data me yawa da kudi kadan a layin ka na MTN.

Yadda zaka sayi 1.5GB data akan Naira 300 a layin MTN

  • Domin samun wannan data me sauki abunda ake bukata kayi shine danna *121*1# akan wayar ka.

Bayan wannan za kaga tsare-tsaren data masu sauki wadanda kake da daman mora, mafi yawa yana farawa ne da 1GB, 1.5GB, 2GB akan Naira 200, 300, 500 a jere da dai sauran tsare-tsaren sayan data masu sauki.

Kana da daman duba tsare-tsaren gaba dayan su idan ka dannan *121# akan wayar ka sai ka zabi Topdeal4Me daga cikin zabin da zasu baiyana maka.

Ka zabi tsarin datan da kake bukatan saya sai kaci gaba da hawa yanan gizo domin kashe kwarkwatan idanu.

Zaka iya baiyana mana a comment ko wane data suka baka daman saya, ka samu me sauki ko dai basu baka dam aba?

Wannan rubutun ya amfane ka?

Turawa abokan ka domin ta yiwu daga cikin su akwai masu bukatan sanin yadda ake karban bashin kudin kira a layin MTN, taimaka musu ta hanyar tura musu link na wannan rubutu ta watsapp, facebook, ko twitter.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button