Right click, Left click da yanda ake amfani dasu ga dan koyo


Right click, Left click da yanda ake amfani dasu ga dan koyo
Right click da left click ba sabo ko bakon kalma bane ga ma’abota amfani da na’ura mai kwakwalwa wato computer domin yana daga cikin abubuwan da ake fara koyarwa sabbin shiga a harkan koyon computer.
Wadannan abubuwa guda biyu suna da bambanci amma mafi yawa idan kaji an ambaci left click za kaji ance right click saboda a jere suke kai bama a jere ba domin kusan guri daya suke sai dai kawai left click yana gefen hagu ne right click kuma yana gefen dama kamar yadda sunan su ya baiyana hakan dai suke.
karanta yanda ake mayar da PDF zuwa Word: https://absanresource.com/2022/05/05/yanda-zaka-converting-pdf-file-zuwa-word-kyauta-pdf-to-word-converter/
A wanan rubutu zan baiyana muku asalin su da kuma amfanin su, ko da yake indai ka saba zuwa wannan shafin za kasan amfanin su domin abubuwa da dama za kaji ance kayi right ko left click za kaga abu kaza da kaza, toh kenan daga nan zaka iya sanin wasu daga cikin muhimmanci ko amfanin right click da left click.
Kafin muyi nisa cikin bayanin akwai bukatan muyi cikakken bayani akan mouse wanda a hausance wasu suke suke kiran shi da jaban na’ura, dalilin da yasa suke kiran shi da haka shine yana kama da jaba, wannan ne dalilin da yasa wasu suke kiran shi da haka a hausance.

Idan kana amfani da laptop ne, sai kaga dama za kasa mouse domin a laptop din yana hade da mouse din shi yayin da ake kiran gurin da suna mouse pack, duk wani abunda za kayi da mouse za kayi dashi domin a hade yake ba kamar desktop ko kuma nace monitor ba, ba tare da dogon bayani ba nasan wata kila kasan hakan idan kuma dama baka sani ba to yanzu ka sani.
A jikin mouse akwai guraren da ake clicking guda biyu, daya a gefen dama dayan kuma a gefen hagu, click na gefen dama shine ake kiran shi da right click, click na gefen hagu kuma ana kiran shi left click kamar dai yadda na baiyana a sama, na sake nanatawa ne saboda a kara ganewa da kyau.

Amfanin right click da left click
- da right click ake creating folder da chanja sunan folder
- da right click ragewa ko kara girman desktop icons
- ana amfani da left click domin selecting text
- ana amfani da right click domin drag na files
wadannan sune kadan daga cikin amfanin right click da left click, idan ka kasance da shafin za kaci gaba da samun ilimin na’ura mai kwakwalwa a kyauta ba tare da ka kashe ko kobo ba, kai dai ci gaba da kasancewa damu.
Idan kaji dadin rubutun turawa abokan ka domin suma su karu, idan ka tura musu sai ka baiyana mana ra’ayin ka da kuma abubuwan da ka koya a wannan shafin wanda da baka iya ba.
Mun gode