mu koyi computer

Yadda ake chanja sunan folder a computer (Folder Rename)

Yadda ake chanja sunan folder a computer (Folder Rename)

A rubutun mu na baya munyi bayani game da yadda ake kirkiran folder a computer tun daga tushe, a wancan rubutun mun baiyana amfanin folder a computer, ma’anar folder da kuma yadda ake kirkiran folder idan baka karanta ba kayi kokari ka karanta domin zai amfanar.

          Chanja sunan folder bazai taba yiwuwa ba dole sai an kirkiri folder, bayan ka kirkiri folder zai iya yiwuwa baka rubuta masa sun aba ko kuma kuma ka rubutan amma kuma kana bukatan chanjawa watakila saboda wasu dalilai dalilai naka kuma ka manta ko baka san yadda ake chanjawa ba.

          Indai wannan ne matsalar ka to tabbas baka da matsala domin kana inda ya dace, a yau kuma a yanzu matsalar zata kawu da yaddan Allah dalla-dalla zan nuna maka yadda za kasa/chanjawa folder suna.

Dalilai dake sa a chanjawa folder suna

Kamar yadda na baiyana a sama, daga cikin dalilai daka iya sawa a chanjawa folder suna; ko dai bayan an kirkiri fokder ba a sa masa sunan daya dace shiba ko kuma an yanke shawaran chanjawa foldern alkibla.

Duk da baza a rasa wasu dalilai da zasu iya haifar da hakan ba amma dai wadannan sune manyan, ko naka dalilin Ya bambanta da wadanda na baiyana? Baiyana mana a comment box saboda musan dalilin da yasa kake bukatan chanjawa folder suna?

Domin koyon yanda ake hada wireless network a computer karanta wannan: https://absanresource.com/2022/05/05/yanda-zaka-hada-wireless-network-a-computer-domin-yin-browsing/

Yadda ake rubuta sunan folder (folder rename) a computer

Bayan ka bude folder, da zaran ka shiga folder zai baka daman rubutu sai ka rubuta sunan da kake son sawa idan ma music ne ko images ko wani daban sai ka rubuta.

Idan kuma ka riga ka kirkiri folder da wani suna na daban kuma kana so ka chanja wannan suna zuwa wani sunan na daban ga yadda za kayi;

  • Ka nemo folder, akan desktop yake kp document? Ko ina yake ka nemo shi sai ka dora cursor akan shi
  • Bayan ka dora sai kayi right click kana yin haka zai nuna maka opions masu yawa sai ka duba can ta wurin karshe za kaga “Rename” sai ka shiga
  • Idan ka shiga Rename nan take za kaga yayi highlight ko kuma select na rubutun dake rubuce a matsayin sunan foldern kawai sai ka rubuta sunan da kake bukata.
  • Idan ka gama rubutawa sai ka clicking gefe ko kan foldern shikenan za kaga sunan daka rubuta din ya baiya a jikin folder naka.

Ko kuma kabi wannan hanya domin chanja sunan folder a na’urar computer

  • Kazo kan folder dakake bukatan chanjawa suna
  • Ka clicking dab kan sunan dake rubuce akan folder zai baka daman rubutu, ka rubuta sunan.

Wadannan sune hanyoyin da zan baiyana domin chanjawa folder suna a computer.

          Ci gaba da ziyartan wannan shafi domin samun ilimi me yawa game da na’ura me kwakwalwa wanda zaka koyi abubuwa da dama hark a kware ba tare da ka kashe ko Naira ba.

          Ko ka karu da wannan rubutu?

Tura shi zuwa ga abokan ka domin suma su karu, sannan kuma hakan zai kara mana karfin gwuiwan ci gaba turo muku rubuce-rubuce masu zafi domin samun Karin ilimi me yawa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button