mu koyi computer

Yanda ake bude sabon folder a computer cikin sauki

Yanda ake bude sabon folder a computer cikin sauki

Mai karatu barka da zuwa wannan shafi me tarin albarka wanda yake kawo da koyar muku abubuwa masu yawa yawa musamman dangane da abubuwan da suka shafi na’ura me kwakwalwa da sauran bangarorin kimiyyar zamani da sauran su

Bude folder a computer abu ne da zai iya kama duk wani mai amfani da computer ko da a lokacin baya zato ko tsammani ne.

Kana koyon computer ko kana bukatan sanin yadda zaka bude folder akan na’urar ka ta computer?

Ka sayi computer amma baka iya aiki da ita ba?, tabbas kazo inda ya dace domin a wannan shafin kadai zaka koyi computer kuma ka kware ka zama oga har ka fara koyarwa matukar kana da bukatan hakan, kai dai kasance dani kawai.

Cikin wannan rubutu zan nuna maka yadda zaka kirkiri folder folder cikin saukin a computer wand aba wai bude folder kadai zaka koya ba a’a duk wani bayanin daya kamata ka sani game da folder zaka sani a wannan shafi idan Allah ya yadda.

Daga cikin abubuwan da zan fara bayani game da creating folder a computer akwai akwai ma’anar ita folder karankan ta domin ina ta cewa folder ta yiwu wani yana bukata yasan wai menene folder?, bayan wannan za mu baiyana amfanin folder da dai sauran su, yanzu kam sai ka gyara zama domin zamu tsunduma cikin karatun ba kakkautawa.

Karanta yadda zaka ragewa computer shan data: https://absanresource.com/2022/05/05/yanda-zaka-rage-shan-data-a-computer-windows-10-auto-update/

Menene Folder?

Folder zamu iya kiran shi da matattara, ma’ajiyan (ko wasu kalmomin masu da wadannan) bayanai wanda ya kunshi rubutu, video, audio, pdf, audio, hotuna da matara Kaman su.

Wato a cikin wannan bayanin zamu fahimci cewa folder dai ajiya a keyi a ciki kuma abubuwan da ake ajiyewa a cikin sune hotuna, video, music da sauran su, a takaice folder zamu iya kiran shi ma’ajiyan bayanai. Me yasa na kira shi da ma’ajiyan bayanai? Saboda ana ajiyan bayanai a cikin ta.

          Akan na’ura mai kwakwalwa (computer) ana adana video, PDF, rubutu (word), hotuna da sauran su. Zaka iya bude folder mai suna images ko hotuna sai ka ajiye duk hotunan dake kan kwamfutar ka a cikin wannan folder, haka za kayiwa music ka bude folder me suna music sai ka zuba duk music dake kan computer zuwa wannan folder. A takaice dai bisa ga wadannan bayanai masu tsayi nasan ka fahimci abunda ake kira folder yanzu kuma zan sake bada misali guda daya kuma shine na karshe domin ka kara fahimtar abunda ake kira folder a computer.

          Ko a cikin wayar ka akwai foldodi wadanda ka adana ko ka ajiye abubuwan dake kan wayar ka a ciki, misali receive duk kankanta waya indai tana da Bluetooth toh ana samun wani abu me suna received a cikin ta wanda duk abunda aka tura yana zama ne a receive, wannan received in folder ne, haka cool music, cool video, cool photos duk waddannan sunan su folder, na tabbata yanzu kasan meye folder to bari mu antaya zuwa gaba kuma.

Amfanin folder akan computer

Folder yana da amfani sosai zan baiyana wasu daga ciki:

  • Zai hana cunkushewan files akan computer, idan a kayi aiki sai ya kasance ba a saving a folder musamman idan a desktop ake ajiyewa zai cike kuma zai kasance babu dadin gani.
  • Bambance files dake kan computer misali wannan folder ne na hotuna wancan kuma na audio ko video da sauran su.

Yadda ake creating folder a system (computer)

Bayan ka kunna computer ka iso kan desktop ga matakan da za kabi domin bude folder:

  1. Da farko za kayi right click, zai nuna maka options masu masu yawa sai ka duba da kyau za kaga inda aka rubuta “New” jawo jaban na’urar ka zuwa kai (cursor)
  2. Bayan kazo kan New nan ma zai baka abubuwa masu yawa za kaga “Folder” sai ka taba kan shi.
  3. Da zaran ka taba zai baka Daman rubutu sai ka rubuta sunan da kake bukatan sa masa.

Shikenan mun kammala kirkiran folder cikin ‘yan sakanni kalilan, da fatan an karu?

Zaka iya baiyana mana ra’ayin ka ko bamu shawara akan tsarin gudanar da wannan shafin ko kuma ta yadda zamu kara inganta shi a akwatin tsokaci (comment) ko kuma ta adireshin email din mu.

Idan kaji dadin wannan rubutu ka turawa abokan ka domin hakan zai kara mana karfin gwuiwa muci gaba da rubuce-rubuce masu fa’ida domin mu gudu tare mu tsira tare. Mun gode.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button