Labarai

Yanda ake duba Admission a JAMB Portal (Check JAMB Admission)

Yanda ake duba Admission a JAMB Portal (Check JAMB Admission)

Kafin tafiya tayi nisa zan bukaci baiyana ma’anar JAMB domin kar muyi tuya mu manta da albasa, ta yiwu wani ya manta ko kuma bai ma san ma’anar ta ba shiyasa naga dacewan na baiyana cikakkiyar ma’anar domin an takaice sunan ne (abreviation) sai ake kiran ta da JAMB da manyan bakake, JAMB na nufin joint admission and matriculation board.

wani babban abun farin ciki shine da wayar ka zaka iya duba admission a JAMB Portal cikin kankanin lokaci matukar dai kana data a layin dake wayar.

Kana bukatan tafiya makarantar gaba da sakandare?

Ka zana jarabawar JAMB kuma ka samu maki (JAMB cut off marks) da ake bukata kafin a samu admission

Yanzu abunda kake jira kawai shine samun admission ko akasin haka, kuma bakasan yadda zaka duba ba, hakane?

Idan hakane tabbas kana inda ya dace domin cikin wannan rubutu zan baiyana maka yadda zaka duba admission status din ka a JAMB portal kyauta ba tare da ka biya ko naira ba.

Sanin kan kane cewa idan kaje gurin masu dubawa sai ka biya su kudin dubawan, kana da babban waya a hanun ka me zai hana ka dubawa da kan ka? Data kawai kake bukata sai ka shiga Portal na JAMB ka duba shikenan ka checi kudin ka kuma ka samu Karin ilimi.

JAMB tayi gyara a portal din ta yayin da a yanzu haka masu Direct Entry (DE) da Unified Tertiary Matriculation Examination (UTME) zasu iya duba admission din su nako wane shekara. Duba admission status a JAMB portal kyauta.

Batu na gaskiya wasu daga cikin makarantun gaba da sakandare basa fitar da da admission a portal ko notice board din su akan lokaci. Wadanda suka nemi irin wadannan makarantun basu da hanyar duba admission me sauki kamar duba JAMB portal.

Yanda ake duba JAMB result: https://absanresource.com/2022/05/05/yanda-zaka-duba-result-din-ka-a-jamb-portal-check-jamb-result/

Yadda Ake Duba Admisson Status A Jamb Portal

Ga wadanda basu da account na JAMB musamman daga 2016 yayi kasa, akwai bukatan su kirkiri account kafin ci gaba da duba status na admission din su.

Idan kuma kana da profile din JAMB sai kabi matakan dake kasa domin duba admission status din ka a JAMB portal.

1. ka shiga portal na JAMB (joint admission and matriculation board) E-facility ko ka shiga wannan link https://portral.jamb.gov.ng/efaclity.

2. kayi login na account din ka na JAMB (profile) da username da password.

3. bayan kayi login, ka gangara kasa sai ka duba inda aka rubuta check admission status sai ka shiga

4. ka zabi shekaran da ka rubuta jarabawan ka sai ka rubuta JAMB registration number na ka a gurin da suka bada daman rubutawa.

5. sai abu na karsheka shiga check admission status domin ganin status na admission din ka.

Abubuwan da zaka gani bayan ka shiga check admission status guda 3 ne, gasu nan a kasa tare da ma’anonin su:

Admission in progress: wannan yana nufin kana daga cikin wadanda zasu iya samun admission domin admission din naka yana kan hanya ne sai dai kawai kaci gaba da dubawa daga lokaci zuwa lokaci domin ganin chanjawan status din zuwa congratulations you have been admitted.

Congratulation you have been offered provisional admission: wannan kuma yana nufin ka samu admission kuma hukumar JAMB ta taya ka murnan samun admission da kayi, yanzu ya rage ka karba ko kaki karba.

Not admitted: wannan yana nufin baka samu admission ba kwata-kwata.

Wanda ya samu admission a JAMB Portal me ya kamata yayi?

Wanda ya samu admission muna bashi shwara da ya dauki wadannan matakai dake kasa:

  • Bayan ka shiga JAMB Profile din ka sai ka shiga CAPS sai ka karbi admission din (Accept) ko kuma kaki karba (Reject).
  • Ka fitar (print) da adimisson letter (JAMB admission letter) bayan ka karbi admission din kuma za ayi amfani dashi a gurin yin rajista (registration).
  • Ka fitar da asalin result din ka (original JAMB result slip).

Me ya kamata kayi idan har yanzu baka samu admission ba?

Idan baka samu admission ba (Not admitted) wannan matakan ya dace ka dauka:

(1) Ka shiga JAMB CAPS domin ka tabbatar da cewa an dora result din ka ko kuma ba a dora shi ba JAMB portal, idan ba a dora ba tabbas zai shafi admission din ka kuma zaka iya rasawa.

  • Ka shiga profile din ka na JAMB
  • Ka shiga admission status
  • shiga Access my CAPS
  • ka shiga My O’level ka duba ko result din ka na gurin, idan babu sai kaje centre na JAMB mafi kusa da kai domin su dora maka O’level din ka

baza ka samu admission ba idan ba kada result a hannu kayi JAMB (awaiting result).

(2) Ka bincika ko an chanja maka bangaren daka cika ne (Course)

yana daga cikin dokoki da ka’idodi JAMB zata iya chanjawa mutum course da ya ciki zuwa wani daban saboda hadakan takaddan kammala makarantar sakandare (combinations).

Yana da kyau ka ka shiga likau (link) na Transfer Approval domin ganin ko an chanja maka bangaren daka cika ne, kuma idan chanja maka a kayi kana da zabi ka karba ko kaki karba.

(3) kayi JAMB da result din da baya hanun ka (awaiting result)

Idan baka da result a hanun ka sai ka chika JAMB da nufin za kayi amfani ne da result na sakandare wanda za kayi a bana to akwai bukatan bayan ka zana jarabawar akwai bukatan ka dawo JAMB portal ka dora result din.

Idan ka manta baka dora ba to fa baza ka samu admission ba domin zasu dauka ba kayi sakandare bane tunda basu gani ba a portal din su.

Idan wannan rubutun ya amfane ka, taimaka ka turawa abokan ka domin musamman na sada zumunta kamar facebook, watsapp, twitter da sauran su suma su amfana.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button