mu koyi computer

Yanda ake rage Hasken screen na computer (Screen Brightness)

Yanda ake rage Hasken screen na computer (Screen Brightness)

 Idan kana aiki da computer musamman da dare sai ya kasance hasken dake kan screen (screen brightness) yayi yawa sosai yana iya cutar da ido, domin gujewa aukuwar matsalan ciwon ido akwai bukatan ragen hasken daga lokacin da duhu ya fara shigowa.

Hasken computer screen yana cutar da ido musamman da dare, yana da kyau a idan duhu ya fara ka rage hasken screen domin bawa idon ka lafiya.

Kana da computer system?

Baka san yadda zaka rage hasken screen din ba?

Toh wannan rubutun na ka ne, musamman don kai a kayi shi, kai dai kasance da wannan shafin domin ci gaba da samun ilimi akan na’ura mai kwakwalwa a kyauta ba tare da mun karbi ko kobon kaba.

Zan baiyana hanyoyi guda biyu ne wanda ake bi a rage hasken screen din computer, wanda kuma duk wanda kabi zai baka abunda ake bukata, za muyi amfani ne da keyboard da kuma akwatin nema (search bar).

Yadda zaka rage hasken screen na computer

1. Domin rage hasken screen na computer ta hanyar amfani da keyboard ga matakan da za kabi:

  • Bayan ka kunna computer
  • Ka duba keys na saman keyboard din ka daga ciki za kaga key wanda aka rubuta f1 har zuwa f12
  • Sai ka duba f2 da f3, f2 ragewa f3 karawa.

Idan kana bukatan kara hasken screen na computer kawai abunda za kayi shine ka danna f3 idan kuma rage hasken screen din kake bukatan yi sai ka danna f2.

Idan computer a kunne take kana danna f2 hasken zai rage idan kuma f3 ka dannan zai karu.

2. Wannan hanyar kuma za kayi amfani ne da da search bar domin binciko gurin d karawa ko rage hasken screen na computer.

  1. Bayan ka kunna computer sai ka shiga gurin searching
  2. Bayan ka shiga sai ka rubuta “change brightness level” sai ka shiga
  3. Idan ka shiga za kaga gurin karawa da ragewan duk a guri daya yake, idan ka ragewa kake so ka taba gefen hagu idan kuma karawa za kayi sai ka taba gefen daman ka.

Wannan sune hanyoyi biyu da ake kara hasken screen na computer wanda nayi alkawarin baiyanawa, kuci gaba da kasancewa damu don samun sabbin rubuce-rubucen mu.

Ko ka samu wani kalubale a yayin karawa ko rage brightness na computer ka? Baiyana mana irin kalubalen da ka fuskanta ko zamu iya sama maka mafita akai.

Wannan rubutun yayi amfani?

Idan kana ganin zai amfanar turawa abokan ka musamman na facebook, watsapp, twitter da sauran su.

Related Articles

2 Comments

  1. Everything is very open with a precise clarification of the issues. It was truly informative. Your site is extremely helpful. Many thanks for sharing!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button