Yanda zaka boye abubuwan da suke kan desktop (desktop icons)


Yanda zaka boye abubuwan da suke kan desktop (desktop icons)
Zaka iya boye desktop icons na kan computer idan bukatan hakan ta taso, ganin cewa baza a rasa wasu abubuwa daka ajiye akan desktop ba kuma kila ma daga cikin su akwai na sirrukan ka, zai yiwu kafi bukatan su a desktop musamman idan baka kammala aiki akan su ba.
Idan documents ka ajiye zaka iya mantawa amma idan a desktop yake zai yi wahala ace ka manta domin duk sanda ka kunna computer zaka gan shi kamar yadda duk wanda yake kusa dai zai iya gani gashi kai kuma baka bukata a gani.
Yanzu dai abunda kake bukatan sani shine yadda zaka boye abubuwan dake kan desktop din ka (Hide desktop icons) ta yadda babu wanda zai ga abubuwan dake kan desktop din ko da yana tare dakai ne, wannan ya kawo k aba? To tabbas kazo inda ya dace domin anan kuma a yanzu zan baiyana maka yadda zaka boye desktop icons din ka ba tare da bata lokaci ba.
kana bukatan koyon cryptocurrency? karanta wannan: https://absanresource.com/2022/05/10/hanyoyin-da-za-kabi-ka-koyi-cryptocurrency-a-saukake/
Menene Desktop Icons?
Desktop icons sune duk abubuwan da auke kan deasktop wannan a takaice shine abunda desktop icons ke nufi, duk wani files dake kan desktop ana iya dunkule su guri guda a kira su da desktop icons.
Yanzu dai ka fahimci menene desktop icons, abunda ya rage ka sani yanzu shine yadda zaka boye desktop icons din ka, yanzu zaka sani saboda kana inda ya dace ne kamar yadda na sanar dakai tun farko.
Yadda zaka boye desktop icons a computer ba tare da ka wahala ba
A yanzu kuma kai tsaye zamu tafi bayani ne game da yadda ake boye icons dake kan desktop a na’ura mai kwakwalwa (computer) wanda kuma shine kaqan darasin namu a wannan rubutu da kake karantawa.
1. da farko za kayi right click
2. bayan kayi right click zabi da yawa zasu baiyana a gare ka (options) sai ka shiga na farkon wanda shine View.
3. bayan ka shiga View, nan ma dai options ne zaka gani wanda a wannan karon kuma a karshe yake desktop icons sai ka taba kai.
4. da zaran ka shiga za kaga duk abubuwan dake kan desktop zasu bace, baza ka gan sub a kwata-kwata.
Bayan sun bace Zan iya dawo dasu kan desktop?
Wannan tambaya ce da wata kila zaka iya yin ta tunda ai dama suna nan kuma kowa zai iya ganin su kwatswam kuma sai suka bace to ina suka tafi sannan kuma zasu iya dawowa ko dai sun tafi kenan?
Eyh zaka iya dawo dasu idan bukatan hakan ta taso, yadda kuma zaka dawo dasu din ba wani abu mai wahala bane domin ta hanyar da kabi suka fece to nan za kabi ka dawo dasu kuma ba wai wani guri suke tafiya ba a’ah suna nan kawai dai an boye sune daga ganin me gani.
Domin dawo da desktop icons zuwa kan desktop kayi right click, shiga view daga nan sai ka sake shiga desktop icons nan take za kaga sun dawo kamar yadda suke da.
Wannan dai shine yadda zaka boye ko baiyana desktop icons a computer, ci gaba da kasancewa da wannan shafin domin koyon abubuwa masu alaka computer da abubuwa masu kama dasu.
Turawa abokan ka, mun gode.
Everything is very open with a precise clarification of the issues. It was truly informative. Your site is extremely helpful. Many thanks for sharing!
Thank you