Yanda zaka Converting PDF File zuwa Word kyauta (PDF to Word Converter)


Yanda zaka Converting PDF File zuwa Word kyauta (PDF to Word Converter)
Kana da rubutu wanda yake a PDF format kuma kana bukatan mayar dashi zuwa PDF sannan kuma baka iya ba?
Ka hau yanan gizo kana binciken yadda zaka mayar da PDF zuwa Word kwatsam sai kaci karo da rubutu na, kar kaji komai domin ba kai kadai bane kake bincike akan wannan dubban mutane ne suke bincike game da yadda zasu mayar da PDF zuwa Word.
Cikin wannan rubutun nayi cikakken bayanin yadda ake converting PDF file zuwa Word, bayan ka gama karanta wannan rubutun zaka iya mayar da PDF din ka ya koma word yadda zaka editing din shi yadda kake bukata.
Duk wani rubutun da aka mayar dashi zuwa PDF ba a iya editing din shi, sai an bi wata hanya an converting zuwa word kafin za a iya karawa ko rage wani abu a ciki.
Ana mayar da rubutu ko document zuwa PDF ne domin a samu saukin karantawa musamman ga masu amfani da wayoyi, idan an typing document ba a mai dashi PDF ba bazai iya budewa ba musamman a kananan wayoyi kuma bazai yi dadin karantawa ba domin ko da bisa kuskure ne za a iya kari ko rage wani abu a cikin rubutun.
Amma idan yana PDF bazai yiwu kawai don ka bude kana karantawa ka goge ko ka kara wani rubutu a ciki ba ko da bisa kuskure ne sai dai idan kana bukatan wani gyara a ciki ka nemi hanyar da ake bi ayi converting PDF zuwa Word.
Abubuwan da zaka lura dasu kafin ka converting file daga PDF zuwa Word
Idan zaka mayar da wani file na PDF zuwa word akwai abubuwan da kake bukata kafin hakan ya yiwu, gasu nan zan baiyana su a kasa:
- Data, da yake za muyi amfani ne da yanan gizo dole akwai bukatan datan da za ayi amfani dashi kafin a cimma gaci.
- Computer ko waya, zaka iya amfani da computer ko waya, domin wani zai iya tunanin ko dai sai da computer a keyi, to bah aka abun yake ba da wayar ka ma zaka iya.
A takaice wadannan abubuwa guda biyu sune zaka mallaka kafin ka iya mayar da pdf ya koma word.
karanta yanda zaka bude sabon folder a computer: https://absanresource.com/2022/05/05/yanda-ake-bude-sabon-folder-a-computer-cikin-sauki/
Yadda zaka editing PDF file cikin sauki (PDF zuwa Word)
- Zaka shiga wannan link https://www.pdftoword.com/
- Bayan ka shiga zai kawo ka wani guri inda za kaga PDF ta gefen dama sai ka shiga
- Kana shiga za kaga abubuwa da dama daga ciki za kaga PDF sai ka shiga
- Ka shiga select your file ka dauko PDF da kake bukatan mai dashi word
- Bayan ka dauko sai ka rubuta Email Address din ka, za kaga misali a cikin box na biyu
- Sai ka shiga convert now dake karshe.
Cikin ‘yan dakika dakan zasu tura maka da rubutun zuwa wancan email address da ka bayar, ka shiga email din zaka same shi a ciki sai ka bude kayi editind da kake bukata sai kayi printing idan da bukatan hakan.
Wannan shine yadda ake mayar da pdf zuwa word domin ayi editing din shi ba tare da tangarda ba.
Wannan rubutun ya amfanar?
Wasu daga cikin abokan ka a shafukan sada zumunta musamman faceboo, whatsapp da twitter zasu iya bukata, taimaka ka tura musu domin su amfana ta dalilin ka.