Labarai

Yanda zaka duba result din ka a JAMB Portal (Check JAMB result)

check jamb result

Result na JAMB ya fito, zana jarabawar JAMB shine matakin farko na shiga makarantar gaba da sakandare a Najeriya musamman kamar su jami’o’i, kwaleji, polytechnics da sauran su.

Zaka iya duba JAMB result din ka da kan ka kuma a kyauta da wayar ka ba tare da amfani da katin da ake kankarewa ba (scratch card)

Wannan sanarwa ce ta musamman ga wadanda suka rubuta jarabar JAMB (Joint Admission and Matriculation Board) cewa a yanzu haka zasu iya duba result din su domin ganin yawan makin (marks) da suka samu.

Zaka iya duba yawan makin da kayi ta yanan gizo (JAMB Portal) ko kuma ta hanyar tura sako (Text Message), domin ganin amsan jarabawar ka ta JAMB kabi matakai da muka zaiyana a kasa:

domin sanin yanda ake dora 0’level result a JAMB portal karanta wannan: https://absanresource.com/2022/05/05/yadda-zaka-dora-result-din-ka-a-jamb-portal-olevel/

Yadda zaka duba JAMB Result din ka a 2021

Domin duba JAMB Score din ka a website din JAMB kyauta ba tare da kayi amfani da scratch ba kabi wadannan matakai guda hudu:

  1. Da farko zaka shiga portal na JAMB bangaren duba result ta wannan link https://portal.jamb.gov.ng/eFacility_/CheckUTMEResults
  2. Zai kawo ka gurin wani dogon akwatin rubutu (box) sai ka rubuta registration number na JAMB ko kuma Email address da kayi amfani dashi a lokacin da kake cike JAMB.
  3. Bayan ka shigar daga kasa za kaga check my result sai ka shiga.
  4. Da ganan result din ka zai baiyana idan sun kammala aiki akai.

Duba JAMB Score ta hanyar amfani da tura sako (SMS)

Duk wanda ya rubuta JAMB zai iya tura sako kai tsaye daga layin da yayi amfani dashi a lokacin da yake cike form na JAMB, zaka tura wannan sakon ta message RESULT zuwa wadannan lambobi 55019. Cikin kankanin lokaci zasu turo maka da sakamkon jarawar ka na JAMB ta message

Kafin ka tura sakon ya kasance akwai kati a layin wayan na ka a kalla kamar Naira 50 (#50 airtime).

Shin ko ka duba naka? Turo mana makin (marks) daka samu a comment

Wannan rubutun ya amfanar? Idan kana tunanin zai amfanar turawa abokan ka domin su amfana.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button