Cryptocurrency

Yanda ake gane farashin coin zai tashi ta hanyar amfani da coinmarketcal

Yanda ake gane farashin coin zai tashi ta hanyar amfani da coinmarketcal

Yanda ake gane farashin coin zai tashi ta hanyar amfani da coinmarketcal

Yanda ake gane farashin coin zai tashi ta hanyar amfani da coinmarketcal, Coinmarketcal shine coinmarket calendar, daya ne daga cikin manyan shafukan yanan gizo da ake baiyana labarai daban-daban na abubuwan da zasu faru  Kauwan crypto.

Shin kana bukatan fara trading cryptocurrency amma ba kasan ta wace hanya za ka fara ba?

to wannan rubutun na ka ne domin zaka samu hanya mafi sauki da za kana yin trading cryptocurrencies

mun yi bayani ne a kan coinmarketcal domin suna baiyana abubuwa da dama da zasu faru da coin ko token, kuma yana tasiri a gurin tashin farashin cryptocurrencies.

Bincike shine matakin nasara a cryptocurrency

Duk wani abunda zai gudana a kan wani project zaka iya samun shi a coinmarketcal, kuma suna baiyanawa da kwanan watan da za a gudanar.

Misali idan za ayi listing coin a wata exchanger, ko za ayi launching na wani sabon coin/token a kasuwa, coinmarketcal zasu iya baiyanawa kafin ranar da za a liting ko launching din.

Ganin cewa farashin coin na iya kara haurawa zuwa duniyar moon idan za a dora shi musamman a babban exchanger, idan kana bibiyan coinmarketcal zaka iya cin karo da wani coin da za a sa shi a binance idan kayi bincike ka tabbatar da ingancin shi sai ka saya kafin ya shiga binance.

YADDA ZA KAYI AMFANI DA COINMARKECAL

Domin fara amfani da coinmaketcal zaka shiga wannan link https://coinmarketcal.com/en/

Bayan ka shiga za kaga coins da events da lokacin da za a gudanar dashi, taba kan sunan coin din za kaga cikakken bayani tare da link na coinmarketcap domin yin bincike kafin saya idan da bukata.

Lokacin da ya dace ka sayi token

Yana da kyau ka sani cewa ba ko wane lokaci bane zaka fadawa coin ko token ka zuba mishi kudi kawai saboda za suyi event.

Wani event din za kaga saura kwana 1, 2 ko 3 a yi shi, to wane lokaci ne zai fi dacewa ka saya?

Lokacin da yafi dacewa ka sayi coin shine idan ya kasance kamar saura sati biyu a yi event

Lokacin sayarwa kuma kafin ranar event, saboda lokacin ne mafi yawan traders suke sayarwa

da zaran ranar event ya iso farashin token din zai iya yin kasa.

ME YA KAMATA KAYI BAYAN KA SAMU COIN DA ZA SUYI WANI EVENT?

abubuwan da za kayi bazai wuce guda biyu ba bayan ka samu wani token da za suyi wani event mai muhimmanci.

Fundamental analysis

domin tabbatar da ingancin ko wane irin token/coin da zaka saya kana da bukatan yin fundamental analysis domin ka tabbatar da cewa yana da inganci.

idan ba kayi masa fundamnetal analysis baza ka iya sanin yaya ingancin token din yake ba ko da kasa kudi ka saye shi za a iya cewa ka sayi gaibu.

amma idan kayi bincike nan ne zaka fahimci ingancin token ko coin, daga cikin abubuwan da zaka duba akwai karfi da kwarewan team, tokonomics, white paper, abubuwan da mutane suke fada akan project din musamman a social media kamar twitter, telegram da sauran su.

Technical Analysis

bayan kayi wa coin fundamnetal Analysis abu na gaba da ake bukata shine kayi technical analysis domin kasan ta inda ya kamata ka shiga coin, inda zaka fita da sanin yawan riban da zaka samu ko faduwa.

ko baka kware ba zaka iya amfani da support and resistance.

NOTE: wannan ba financial advice bane kar kawai kaga coin kaje ka saya ba tare da kayi bincike ba, ko wane event kaga za a yi na wani project kaje kayi bincike tukuna ka tabbatar da ingancin sa. baza mu dauki alhakin asaran da zai iya biyo baya ba domin akwai hadari sosai a kasuwancin crypto.

wannan rubutun ya amfanar?

turawa abokan na facebook, watsapp da telegram

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button