mu koyi computer

Yanda zaka hada wireless Network a computer domin yin browsing

Yanda zaka hada wireless Network a computer domin yin browsing

Kana bukatan sanin yadda zaka hada wireless Network a computer ka? Kana da computer kuma kana bukatan hada Network amma baka san yadda za kayi ba?

Kana da computer kuma kana so kayi bincike (browsing) a yanan gizo amma baka san hanyar da ake bi a hada network ba, lallai kazo inda zaka koya domin a wannan rubutu zan baiyana maka hanyar da ake bi a hada network a computer domin gudanar da harkokin yanan gizo a computer.

Idan kana da waya ko computer sai kake bukatan hawa yanan gizo domin bincike ko hawa shafukan sada zumunta na zamani kamar facebook, instagram, watsapp da sauran su, bazai yiwu ka fara amfani dasu ba har sai kana da network connection.

Wani zai iya cewa ko dai Magana nake akan data? A’ah ko da kana da data matukar babu network bazai yiwu kayi amfani da yanan gizo ba, tabbas wannan haka yake mutumi na, da yake Magana muke akan akan computer na ambaci sunan waya ne a matsayin misali domin shi ma bazai yiwu kayi amafani da yanan gizo ba matukar babu network.

Amfanin Network

Network yana da matukar muhimmanci hatta ga rayuwar ‘yan Adam domin a yanzu hatta kasuwanci mutane da dama sun sun koma ta network, a yanan gizo za ayi cinki a biya kuma a aikawa wanda ya saya har inda yake, zai yiwu ayi amfani da yanan gizo ba tare da network ba?

Tabbas a’ah za kace to ashe kenan duk kasuwanci da a keyi da yanan gizo ana cin albarkacin network ne domin idan ba network ba yanan gizo idan, bayan kasuwanci ana watsa labarai a yanan gizo wanda shima dai daya ne daga cikin amfanin yanan gizo.

Amfanin network bazai kididdigu ba sai dai kawai a lissafa wadanda suka sauwaka kuma nima anan zan dakata domin nasan kasan muhimmancin yanan gizo a wannan zamani da kusan komai ana iya yin shi a networkance.

Hanyoyin hada Network

Ganin cewa hanyoyin hada network a computer suna da yawa domin akwai wireless da non wireless sannan kuma su din ma hanyoyin hadawan yana da yawa

Kafin na tafi bayani kai tsaye kan yadda za a hada wireless network din zan yi bayani kadan akan wireless da non wireless network domin a fahimce su sosai kar muyi tuya mu manta da albasa.

(i) Wireless network shine network wanda ake hada shi ba tare da anyi amfani da waya ba, kamar USB cable kenan da dukkan sauran nau’oin waya.

(ii) Non wireless network kuma shine network din da aka hada shi tare da waya, kamar USB cable da sauran dangin wayoyin hada network

karanta yanda zaka ragewa computer shan data: https://absanresource.com/2022/05/05/yanda-zaka-rage-shan-data-a-computer-windows-10-auto-update/

Yadda ake hada wareless network a computer

Kamar dai yadda na baiyana hanyoyin hada network suna da yawa sannan kuma zan yi bayani ne akan wireless wanda ake amfani da waya domin hada network a computer

1. da farko zaka bude datan wayar ka da host pot

2. bayan kayi wannan sai ka bude wifi na kwamfutar ka

3. da zaran ka bude za kaga ya fara searching

4. bayan ya gama searching sunan wayar ka zai baiyana sai ka taba kai za kaga connect.

5. da zaran ka taba connect za kaga ya fara searching can zai nuna maka connect shikenan ka hada network sai kaci gaba da browsing din ka da sauran abubuwan da kake bukatan yi a yanan gizo.

Abubuwan da zaka lura dasu kafin connecting wireless network

Kafin ka fara hada wireless network da wayar ka dole sai ka mallaki abubuwa kamar haka:

1. wayar android

2. layin waya

3. Data

Wadannan sune muhimman abubuwan da zaka mallaka domin hada wireless network a kwamfutar ka.

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button