mu koyi computer

Yanda zaka rage shan data a computer windows 10 (Auto update)

rage shan data a computer

Yanda zaka rage shan data a computer windows 10 (Auto update)

Kana amfani da computer wanda windows 10 a kan ta?

 Kana fuskantar matsalan karewan data da wuri?

Da zaran ka sayi data bazai dau wani lokaci me tsayi ba sai ya kare, ka nemi yadda zaka magance matsalan shanyewan data da wuri a computer ka amma har yanzu baka samu solution ba.

Toh wannan matsalan dai ba abun damuwa bace yance yanzu domin kazo inda za a magance maka ita cikin kankanin lokaci kuma a kyauta ba sai ka biya mu ba.

Kila kayi bincike sosai akai har kana jin nauyin ci gaba da tambaya, toh ai ba damuwa bane wannan domin wadanda suke bincike akai suna da yawa kuma ma baza su kirgu ba domin mutane da dama suna fama da matsalan karewan data da wuri a computer da suke aiki da ita.

Bari dai na takaice maka ko nima nan da nake maka bayani a lokacin da na fara amfani da windows 10 a computer na nayi fama da irin wannan matsalan, idan na sayi data bazai dade ba sai ya kare.

Zan sayi data mai yawa wanda nake tunanin zai min kwanaki sai naga wani lokacin yak are ba a lokacin da nake tsammani ba, nayi bincike sannan kuma na tambayi kai na wai menene matsalan? Shin ko dai bani kadai nake amfani da datan ba shiyasa yake karewa da wuri?

Na kasa bawa kai na amsa saboda dai tun kafin nayi tambayar nasan cewa ni kadai nake amfani da data na sai dai kawai saboda na rasa dalilin zuqewan datan ne yasa nake tambayoyi kala-kala wai ko zan samo mafita ko kuma dalilin shanyewan datan da wuri.

Na dau lokaci me tsayi kafin na samu mafita ashe daga windows 10 ne, da yake sabon fitowa ne (updated) kuma an kayatar dashi fiye da sauran windows sannan kuma an saka mishi wasu abubuwan da sauran windwos na da basa dashi musamman windows 7 da a kafi amfani dashi.

KARANTA YANDA AKE CHANJA SUNAN FOLDER A COMPUTER: https://absanresource.com/2022/05/05/yadda-ake-chanja-sunan-folder-a-computer-folder-rename/

Yadda zaka dakatar da Auto Update a Windows 10

  1. Akan keyboard din computer, ka dannan ‘windows R’. kamar dai yadda ake control A, control B, haka za kayi, sai dai wannan kuma windows R za kayi.
  2. Wani box zai baiyana a fuskan computer, za kaga ‘services.msc idan kuma baka gani ba akwai wani arrow a jikin wannan box sai ka taba shi zaka gani sai ka shige shi.
  3. Wani window (box) zai sake baiyana sai ka gangara kasa za kaga ‘windows update’ sai kazo kan shi kayi right click.
  4. Ka shiga properties
  5. Da ganan idan ka duba za kaga ‘Starup type’, a gefen shi za kaga wani box da arrow da rubutu kuma a ciki, idan disable ka gani to baya auto update sai ka fita kawai domin bazai zuqe maka data ba, idan bashi ka gani ba sai ka tafi mataki na shida
  6. Ka taba wannan arrow sai ka shiga disable, ka taba stop dake kasa
  7.  Bayan kayi wannan, sai ka taba Apply daga nan sai ka taba Ok.

Shikenan ka dakatar da Auto Update, datan ka bazai na karewa da wuri ba domin ka rig aka magance matsalar.

Me ya kamata kayi idan kana amfani da Windows 10?

Abunda ya kamata kana yi shine duk lokacin da za kayi amfani da data ko kuma daga lokaci zuwa lokaci kana duba Auto Update, idan ba a disable yake ba sai ka mai dashi disable.

Shin ko ka samu nasaran dakatar Auto Update? Baiyana mana a comment domin mu sani ko ya yiwu ko bai yiwu ba, idan da bukatan wani taimako sai mu maka.

Wannan rubutun ya amfanar?

Turawa abokan ka musamman na social media domin suma su karanta su karu, watakila akwai masu fama da matsalan zuqewan data da gaggawa idan ka tura ka taimake su.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button