Cryptocurrency

Cikakken bayani akan Cryptocurrency da abubuwan da ya kunsa

meye ne cryptocurrency?

Cikakken bayani akan Cryptocurrency da abubuwan da ya kunsa

Cikakken bayani a kan Cryptocurrency da abubuwan da ya kunsa; Ganin cewa mutane da dama har yanzu basu fahimci menene Cryptocurrency ba, wannan ne yasa na dau harama domin wayar musu kai a wannan shafi.

Wasu sun shiga Cryptocurrency ne ba tare da sun nemi ilimin shi ba, tabbas hakan babban kuskure ne.

Cryptocurrency kasuwanci ne a yayin da jama’a da dama suka dauke shi a matsayin sana’a a wannan duniya ta mu sai dai ya kasance wasu suna kuka wasu suna farin ciki.

Da ma haka kasuwa ko wace iri ta gada, yau idan kaci riba ta yiwu wata rana ka samu jarabawa ta asara.

Sai dai abun ya sha bamban da crypyo, mafi yawa daga cikin masu tabka asara sun shiga crypto ne ido a rufe ba tare da sun nemi ilimi ba.

Sun ji labari ana samun kudi sai suka shigo kawai da nufin suyi kudi dare daya kuma basu nemi ilimin sanin yanda kasuwan take ba, kaga irin wannan dole ya kasance cikin asara.

Sai dai idan ya taki sa’a zai iya lucky idan yaci nasaran shiga wani coin da yake shirin bayar da kudi wa mutane a dai-dai lokacin da ya shiga.

Mafi yawan wadanda kuma kake gani suke cin nasara a Cryptocurrency sun fara ne da neman ilimin crypto, san nan kuma sai suka kasance da hakurin jurewa kasuwa duk yanayin da suka samu kan su a ciki.

MENENE CRYPTOCURRENCY?

Zaka iya kiran shi da Cryptocurrency ko kuma ka yanke karshen ka kira shi da “crypto” duk wanda kace yayi kuma za a fahimci abunda kake nufi.

Cryptocurrency wani irin kudi ne wanda ba a iya gani ko taba shi, a yanan gizo (internet) ake amfani dashi wanda a ka dora shi a kan fasahan blockchain.

Cryptocurrencies a na iya saye da sayarwa dasu, akwai kamfanunuwa da suka karba a matsayin kudin kaya ko aikin su.

Misali idan zaka sayi riga, wando, agogo da sauran su zaka iya biya da Cryptocurrency.

Bayan wannan zaka iya ajiye Cryptocurrency na ka zuwa wani lokaci da darajar sa zata iya karuwa sai ka sayar kaci riba.

Nasan kana taraddadi ko?

Wata kila ma ka shiga rudani

Kana ta tambayan kan ka wai wane irin kudi ne haka da ba a iya gani ko tabawa sai dai kawai a yi amfani dashi a online?

Wani ma ya fara tunanin wai anya wannan abun gaskiya ne kuwa?

Uhmm toh dan uwa me irin wannan tunanin ko ka taba jin laharin digital currency?

Tabbas na san zaka iya cewa eh ka taba ji domin kasashe da dama suna anfani dashi

Har Nan Nigeria shekaran da ya gabata babban bankin Nigeria wato CBN sun yi kokarin samar da digital currency mai suna E-Naira.

E-Naira shi ma kudi ne amma a internet kadai ake amfani dashi

E-Naira kamar Nairan takadda yake dai dai shi a online kadai ake amfani dashi.

Bambancin kawai shine wannan a takadda yake, takaddan zaka dauka ka bayar a sayar maka da abu.

Wancan kuma ta online zaka tura shi zuwa ga Wanda zaka sayi kaya a gurin shi, shikenan.

Da fatan dai ka fahimta?

MENENE MISALAN CRYPTOCURRENCY?

wasu daga cikin misalan crytocurrencies

bayani akan Cryptocurrency; A yau muna da Cryptocurrencies dubbai, sai dai wanda yafi sanuwa kuma a ka fara cin nasaran samar dashi shine Bitcoin wanda ake kira da BTC.

Sauran cryptocurrencies sun hada da Etherium, BNB, Bitcoin cash, Luna, Solana da sauran su.

Ko wane coin da ka gani yana da amfanin shi domin ana samar dasu ne saboda su warware wata matsalar.

 Cryptocurrency da ka mallaka babu shi a siffan takadda ko kwandala, ba a iya ganin shi sannan a internet yake.

INA AKE AJIYE CRYPTOCURRENCIES?

Wadanda suka sayi Cryptocurrency don su ajiye na tsawon lokaci suna ajiyewa ne a wallet, daga cikin wallet sanannu akwai Trust wallet d.s.

Idan Kuma trading za kayi sai kayi amfani da exchanges, daga cikin manyan exchanges da zaka iya amfani dasu akwai Binance, OKX, kucoin, gate.io da sauran su.

ME A KEYI DA CRYPTOCURRENCY?

kamar yadda muka fara baiyanawa a sama Cryptocurrency ana iya amfani dasu wajen saye da sayarwa sai dai ba ko wane dan kasuwa bane yake karban crypto a matsayin kudin sayan kayan shi ba.

Amma akwai kamfanoni da daidaikun mutane da suke karba, idan kana bukatan sayan kaya ka biya da crypto sai ka nemi inda suke karban crypto.

Ko kuma ka sayar da crypton ka sai ka dawo da kudin zuwa account din ka na banki kaje ka sayi abunda kake bukata kai tsaye.

KARANTA: https://absanresource.com/2022/05/05/yanda-ake-duba-admission-a-jamb-portal-check-jamb-admission/

SHAWARAN DA ZAN BAKA

1. a matsayin ka na sabon shiga crypto ka fara neman ilimi kar ka tsaya sai kaji ana ambatan sunan coin a social media kafin ka saya domin zaka iya tabka asara

Wani coin din sai ya riga ya bada kudi a ke fara ambatan sunan shi a socila media don haka ka bude idon ka da kyau ka shiga crypto a matsayin wayayyen mutum.

2. Kar ka sayi coin din da ya riga ya tashi domin zai iya sauka a ko wane lokaci.

3. Idan trading za kayi, kar kana rena riba domin hausawa su kace da asara gara gidadanci

4. Kar ka karbi bashi a gurin ko waye kasa a crypto, yin hakan zai iya sa ka dana sanin da wata kila baka taba yin irin shi ba.

5. Ko da kudin kane idan za kasa a crypto ka tabbatar baza ka bukace shi nan kusa ba, zaka iya sayan coin sai farashin shi yayi kasa idan kana bukatan kudin dole zaka cire shi duk faduwa zai baka a wannan lokacin.

6. Ka tabbatar kasa kudin da kafi karfin shi, misali ko da a ce zaka iya rasa wannan kudin hankalin ka bazai tashi ba.

shin ka amfana da wannan da wannan rubutun?

idan ka amfana kayi like sannan ka turawa ‘yan uwa da abokan arziki wadanda suke bukatan koyon cryptocurrency.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button