Cryptocurrency

Ma’anar stablecoins a cryptocurrency da amfanin su

Stablecoins a cryptocurrency da amfanin su

Ma’anar stablecoins a cryptocurrency da amfanin su

Ma’anar stablecoins a cryptocurrency; Cikakken Ma’anar stablecoins da muhimmancin su a cryptocurrency, A duniyar crypto currency akwai abun da ake kira stablecoins wanda ya kamata a ce duk wani dan crypto ya san su kuma zai iya cewa wani a kan su da zaran an tambaye shi.

Kar ka yadda kana crypto ba kasan bayani a kan ire-iren wadannan kalmomi ba domin a ko wane lokaci za a iya tambayar ka domin neman Karin bayani ko kuma dai kawai don a tabbatar da cewa kasan crypto ko dai har yanzu lalube cikin duhu ka keyi?

A cikin wannan rubutu zan yi cikakken bayani a akan stablecoins da abubuwan daya kunsa, don haka ka natsu da kyau kuma ka gyara zama domin ina me tabbatar maka da cewa indai zaka kasance da wannan shafi na absanresource tabbas zaka samu ilimin crypto kyauta.

Ko wane dan crypto yana amfani da stablecoins musamman a lokacin da zai sayi wani coin ko token kuma idan zai sayar da coin ko token da yayi trading ko holding.

Sai dai kuma abun mamaki shine ba kowa ne yasan menene stablecoins ba, duk da yana amfani dashi duk lokacin da zai saya ko Zai sayar da coin.

Me yasa hakan yake faruwa?

Babban dalilin da yasa za kaga mutum yana crypto amma bai san ma’anar stablecoin ba shine yawancin mutane sun fi mai da hankali kawai gurin sanin yanda za suyi amfani da exchanges na cryptocurrency domin saya da sayarwa.

Amma ba kowa ne ya damuwa da daukan littafi ya karanta domin ya nemi tsagwaran ilimin crypto ba, yin hakan za a iya kiran shi da kuskure domin ba karamin asara yake iya jawowa ba.

Mutane da dama suna kuka saboda irin asaran da suke tabkawa a kasuwan crypto sai dai masu wannan kukan fiye da kaso 70 sun shiga crypto ne ba tare da ilimin sanin hakikanin crypto ba.

Stablecoin yana da muhimmanci sosai a crypto, saboda muhimmancin sa wasu masana crypto suke masa lakabi da suna “kashin bayan crypto”

Kuma idan ka duba za kaga lallai maganar su haka yake, idan da a ce ba stablecoins a crypto to da asaran da za a yita tabkawa a Allah ne kadai ya sani

MENENE STABLECOIN A CRYPTO?

Idan a kace stablecoin ana nufin duk wani coin wanda a ka samar dashi musamman domin yayi kafada da kafada da kudin wata kasa.

Ya kasance farashin wannan stablecoin yana dai-dai da farshin kudin kasar, kamar yadda kudin kasar baya hawa ko sauka toh haka shima stablecoin yake baya hawa ko sauka.

Sabanin sauran coins da ake saya domin su tashi su bayar da riba a sayar a cire kudin zuwa account na banki, su stablecoins a tsaye suke guri daya.

To ya kake gani idan ka shiga cryptp ba tare da ilimi ba sai ka sayi stablecoin da nufin ya baka riba? Zai kasance kamar jiran gawon shanu kenan.

MEYE MISALAN STABLECOINS?

A crypto muna da stablecoins da dama amma masi shahara a cikin su ko kuma nace wadanda mu kafi amfani dasu a nan sune kamar haka; USDT, BUSD da sauran su.

Dukkan su farashin su daya ne da dalan Amurka.

Bari na baka misali yanda zaka gane.

Yanda stablecoin yake shine;

Stablecoin daya yana dai-dai da dalan amurka daya.

Zai kasance kamar haka;

1 USDT = $1

$1 = 1USDT

1 BUSD = $1

$1 = 1 BUSD

Kamar yanda na baiyana a sama stablecoins suna da yawa na bada misali ne da wadanda mu kafi amfani dasu.

Us dollar

MUHIMMANCIN STABLECOINS A CRYPTOCURRENCY

Stablecoins yana da matukar muhimmanci a crypto, ga wasu daga cikin amfanin stablecoins:

  • Idan an shiga DIP zaka iya mayar da asset din ka stablecoin saboda gudun asara
  • Ana saye da sayar da coins dasu
  • Zaka iya staking din shi domin samin commission
  • Zaka iya zama merchant a P2P kana sayarwa kana samun riba

Wannan wasu ne daga cikin amfani ko muhimmancin stablecoins.

da fatan ka amfana da wannan rubutu?

kayi sharing musamman wa abokan ka wadanda suke bukatan neman ilimin cryptocurrency domin suma su amfana kuma susan hakikanin abunda ake nufi da stablecoins.

Mun gode.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button