Cryptocurrency

Hanyoyin koyon cryptocurrency a saukake

koyon crypto

BAYANI A KAN HANYOYIN DA MUTUM ZAI BI YA KOYI CRYPTO

Hanyoyin koyon cryptocurrency a saukake, Shin ko kana daya daga cikin mutenen da suke so su shigo harkan kasuwancin zamani na cryptocurrency kuma ba kasan ta ina zaka fara ba?

Idan kana cikin su ina taya ka murna domin a yanzu haka kazo inda ya dace

A cikin wannan rubutu zan baiyana maka hanyoyin da za kabi ka koyi crypto har ma ka kware matukar ba kasa wasa ba a harkan.

Cryptocurrency kasuwanci ne wanda ake samun kudi dashi fiye da tunanin ka, indai zaka shige shi tare da ilimi zaka sha mamaki saboda irin alherin da zaka samu.

Kafin mu tafi kai tsaye zuwa ga hanyoyin da za kabi ka koyi cryptocurrency yana da kyau mu san menene cryptocurrency shi karan kan shi.

Ta yiwu yau ne ka fara karanta rubutu a kan crypto, idan hakane tabbas za kaso kasan me ake nufi da crypto kafin kasan hanyoyin da za kabi ka koyi kasuwancin crypto.

MENENE CRYPTOCURRENCY?

Cryptocurrency kudi ne wanda yake kan internet kuma a internet din kadai ake amfani dashi ba kamar irin kudin mu na takadda ba.

Kudin crypto ba a iya ganin shi da ido

ba a iya taba shi

akan internet yake

a internet ake amfani dashi.

Wannan shine cryptocurrency a saukakakken harshe

Sai dai kuma akwai wadanda suke a matsayin kadara, zaka saya ka ajiye idan wata bukata ta kama ka zaka iya sayarwa domin biyan bukatar.

KARANTA: cikakken bayani akan cryptocurrency

ME A KEYI DA CRYPTOCURRENCY?

Ana yin abubuwa da dama da kudin internet na crypto, zan baiyana wasu daga ciki;

  • Ana sayan kaya da crypto
  • Ana ajiye shi na tsawon lokaci domin a samu riba mai yawa
  • Ana saye da yasarwa da kudin crypto

MENENE HALIN CRYPTO?

Crypto yana da wani hali guda daya sananne wanda ko yau ka fara koyon crypto zaka iya sanin wannan halin na shi.

Daga cikin manyan halayya na crypto akwai volatility.

Menene volatility?

Volatility shine hawa da saukan farashi, cryptocurrencies suna da saurin hawa da sauka shine ake kiran kasuwan da high volatile market.

Shiyasa aka samar da stablecoins, idan kasuwa zata shiga DIP ko coin da ka saya ya fara nuna alamun zai yi kasa sai ka mayar da coin din ka ya koma stablecoin saboda gudun asara musamman idan trading ka keyi.

Hanyoyin koyon cryptocurrency a saukake

Hanyoyin koyon cryptocurrency

Sanin hanyoyin da za kabi ka koyi crypto ne muhallu shahid na wannan rubutu, nayi bayanin dake sama ne saboda na kara fito da abun a fili domin crypto yana da fadi sosai.

Abu na farko shine neman ilimi

1. ka nemi wani masanin crypto a unguwar ku ko garin ku ya koya maka.

Daga cikin matsalolin da ake samu a crypto shine yawan asara, mutum zai iya sa kudi ya sayi wani coin ko token daga karshe sai yayi asara maimakon riba.

Babban dalilin da yake kawo haka shine rashin neman ilimi, idan baka nemi ilimi ba daga farko zaka iya asaran duk abun da kasa a dan karamin kuskure.

2. idan haka bai samu ba, ka nemi makarantar da a ke koyarwa a online.

Akwai makarantu da dama da suke koyar da crypto a online tun daga kan na turanci har zuwa harshen mu na hausa.

Zaka iya hawa browser na wayar ka kayi bincike domin samun wata makaranta ka shiga kayi karatu daga matakin farko zuwa kwarewa.

3. ko kuma kaje youtube ka binciki channel da suke koyar da crypto

A youtube akwai channels masu yawa wadanda suke koyar da tsantsan ilimin crypto.

Idan baza ka samu daman cire kudi ka biya ba zaka iya zuwa youtube ka nemi channel da suke koyar da crypto ka fara koya a can.

4. kayi abota da ‘yan crypto musamman wadanda suka fika sani

A social media kamar su twitter, facebook akwai manyan masana ilimin crypto wadanda suke rubuce-rubuce a ko wane lokaci.

Su ma idan kana bibiyan su zaka kara samun gogewa a kasuwar.

5. ka kasance me yawan bincike

Idan kana so kaci nasara a crypto dole ne sai ka tsaya da kafan ka, baza ka iya tsayawa da kafan ka sai ka kasance me yawan bincike.

Kar ka tsaya kana jira wai wani ya kawo maka sunan wani coin ka saya, a’ah kayi kokari ka zama me kawowa.

Jira a fada maka coin ba ina nufin laifi bane sai dai kawai yana da kyau duk lokacin da a ka fada maka sunan wani coin kar kaje ka zuba mishi kudi kawai kai tsaye, kayi naka binciken tukun.

Bincike shine matakin nasara a crypto.

Wadannan hanyoyin idan kayi kokari ka daure kabi su tabbas zaka koyi crypto har ma ka koyar da wasu.

Dole ne ka cire ganda da lalaci matukar kana bukatar cin nasara a harkokin kasuwancin ka na crypto.

Mafi yawan asaran da a keyi a crypto rashin kwakkwaran bincike ne yake haifar dashi, saboda haka yana da kyau kayi kokarin farawa tun daga yanzu, ba anjima ba fa, a’ah ka fara yanzu.

Wannan rubutu na Hanyoyin koyon cryptocurrency ya amfanar da kai?

Shin ko kana da abokai wadanda burin su shine su koyi crypto?

Idan hakane me zai hana ka nuna musu wannan shafin domin su samu gurin kara fadada ilimin su na crypto?

Ka yiwa abokan ka sharing domin su ma su karu.

Shin ko kana da wata tambaya ko neman Karin bayani a akan cryptocurrency?

Kofar mu a bude yake domin taimakawa a ko da wane lokaci

Turo mana ta comment a karkashin wannan rubutu, mu kuma zamu amsa maka tambayar ka da zaran ya iso gare mu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button