Labarai

Sakamakon jarabawar JAMB na 2022 ya fito?

Jamb result

Sakamakon jarabawar JAMB na 2022 ya fito?

A matsayin ka name shirin tafiya jamai’a a Nigeria dole ne sai ka zana jarabawar JAMB

Ko kana daga cikin wadanda su kayi JAMB a wannan shekarar?

Tabbas zai iya kasamcewa kana cikin kokwanto na an sake jarabawar ne ko dai ba a sake ba?

A satin da ya gabata ne a ka fara rubuta jarabawar JAMB na shekara ta 2022.

Tun daga daren shekaran jiya litinin wanda yayi daidai da 9/05/2022 jita-jita ya fara yawo na cewa jarabawar JAMB ya fito

Toh wai shin gaskiya ne jarabawar ya fito ko dai labarin kamzon kurege ne?

Wannan shine abunda zamu tattauna a cikin wannan rubutu da kake karantawa a yanzu.

SAKAMAKON JARABAWAR JAMAB NA 2022 YA FITO?

Dalibai da dama sun fara korafi ganin cewa Yau kusan kwana 5 kenan da fara zana jarabawar amma sakamakon bai fito ba.

sai dai kuma a wani bangaren hukumar JAMB ta tabbatar da cewa a yanzu haka tana gab da sakin sakamakon

Hukumar ta JAMB taci gaba da cewa dalilin da yasa ba a sake sakamakon ba har yazu shine suna ci gaba da bincike ne domin tabbatar da ingancin jarabawar da a ka gudnar kafin su sake.

Har ila yau hukumar taci gaba da cewa tana binciken na’urorin CCTV ne wanda a ka kafa a guraren zana jarabawar don tabbatar da sahihancin jarabawar.

Daga karshe hukumar tayi barazanan soke jarabawar duk wani dalilin da a ka samu yana satan amsa a yayin gudanar da jarabawar JAMB na bana.

Hukumar JAMB ta fitar da wannan sanarwa ne a ranar talatan nan data gabata.

kuci gaba da kasancewa da wannan shafi domin samun sabbi da ingantattun labarai da suka shafi JAMB

kayi sharing wannan labarin domin sauran dalibai su amfana.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button