Airtime Offer

Yanda zaka samu Bonus na kudin kira a tsarin MTN 10X Bonus

Yanda zaka samu Bonus na kudin kira a tsarin MTN 10X Bonus

Yanda zaka samu Bonus na kudin kira a tsarin MTN 10X Bonus

mai barkatu barka da zuwa Absan Resource, a yau za muyi bayani ne akan yanda zaka samu Bonus a layin MTN

Daga lokaci zuwa lokaci kamfanin layin sadarwa na MTN suna fitar da garabasan katin kira (airtime) ko na data

A wannan lokaci MTN sun fito da wani garabasa wanda zaka samu katin MTN har kashi goma na abun da kasa

Nasan zaka iya yin mamakin jin haka, to wannan ba abun mamaki bane domin MTN suna da karfin da zasu iya yin fiye da haka.

Ba a kan wannan suka fara kawo sabbin shirye-shiryen da suke kawo sauki wa abokan huldar sub a

MTN sun dade suna kawowa irin wannan tsarin saboda su samu su sake jawo customer a jikin su.

YANDA TSARIN MTN 10X BONUS YAKE

A wannan tsari na garabasan kudin kira da suke bayarwa zaka samu kasha goma ne na abun da kasa kamar yanda nayi bayani a sama.

Bari na baka misali saboda ka fahimta yanda ya kamata.

Misali

Idan kasa katin Naira 100, zasu baka katin Naira dubu daya

Idan kasa katin Naira 200, zasu baka katin Naira dubu biyu

Idan kasa katin Naira 500, zasu baka katin Naira dubu biyar

KARANTA: Yanda zaka samu kyautan lokacin magana na minti 12 a layin Airtel

YANDA  ZAKA SAMU BONUS A LAYI MTN (MTN 10X BONUS)

Wannan tsari da MTN zasu baka kashi goma na kudin da kasa bai da wahala, ga matakan zan baiyana su a kasa;

  • Ka sayi katin MTN
  • Ka shigar da katin ta wannan tsarin; *800*lambobin katin#

Misali idan wannan shine lambobin katin da ka saya 1233445560, ga yadda za kayi

*800*1233445560#

Wannan kati na garaba zai kare ne a cikin kwanaki 30.

Nan take katin zai shiga sai dai kawai ka fara kira domin more garabasan MTN na kudin kira kasha 10 na katin da ka saya.

NOTE: ka tabbatar da lambobin kati kayi amfani, ba zai yiwu kayi amfani da transfer ba.

Shin kana da wata tambaya?

A shirye muke mu baka amsa tambayoyin ka akan wannan tsari na garabasan katin kira da MTN suke bayarwa

Turo tambayar ka ta comment

Mun gode

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button