Yanda ake samun kyautan lokacin kira na minti 12 a layin Airtel (Airtel special offer)


Yanda ake samun kyautan lokacin kira na minti 12 a layin Airtel (Airtel special offer)
Mai karatu Barka da zuwa Absan Resource Blog
Shin ko kana amfani da layin Airtel?.
Kana bukatan sabbin promo da Airtel suke fitarwa domin saukakawa kwastomomin su?
Domin samun sabbin tsare-tsare na layukan sadarwa da muke amfani dasu kasance damu a ko wane lokaci a wannan shafi
Layin Airtel suna da saukin mu’amala hakan yasa birni da kauye ake amfani dasu
A wannan karo ma sun sake fitar da wani sabon tsari wanda zaka samu lokacin magana har na tsawon minti 12
Ka fahimta?
Idan baka gane ba bari nayi maka bayani gwari-gwari yadda zaka fahimta yadda ya kamata.
Magana a kan minti 12, abunda ake nufi a nan shine
Za kayi minti 12 kana yin waya, da zaran mintunan sun cika shikenan wayan zai yanke
ZAN IYA KIRAN KO WANE LAYI A WANNAN TSARIN KIRA NA AIRTEL?
Na san wannan tambayar za ta iya kasancewa a cikin zuciyar mai karatu
Dalilin hakan yasa zan amsa ta saboda kar ka wahalar da kan ka wajen neman amsa
Wannan tsarin kiran lokacin magana na tsawon minti 12 da Airtel zasu baka zaka iya kiran ko wane layi dashi, Tun daga kan Airtel, MTN, Glo, Etisalat.
Ba kada matsala ko wane layi zaka iya kira dashi
Wani lokaci a na iya samun tsarin da bazai yiwu ka kira wani layin waya wanda ba Airtel ba amma a wannan tsarin ko wane layi za ka iya kira dashi.
Yanda ake samun kyautan lokacin kira na minti 12 a layin Airtel (Airtel special offer)
YANDA ZAKA SAMU LOKACIN KIRA NA TSAWON MINTI 12 A LAYIN KIRA
Tabbas na san abunda kake jira kenan a dai-dai wannan lokaci domin ka more wannan offer da Airtel suka fitar dashi saboda samun sauki.
Sai dai a wannan tsarin ba lokacin bane kadai ake samu a’ah har ma da data domin ci gaba da hawa yanan gizo.
Riba biyu kenan, ga lokacin magana sannan kuma ga data
KARANTA: Yanda zaka karbi bashin kudin kira a layin MTN
YAYA TSARIN SAMUN DATA DA LOKACIN KIRA YAKE A LAYIN AIRTEL?
Da yake komai da ka’ida yake, wannan tsarin shi ma da na shi ka’idan sai yana da matukar sauki.
120MB data ake samu, sai kuma lokacin magana na tsawon min 12 kamar yanda nayi bayani a chan sama.
Ga yanda zaka samu wanna garabasa;
- Kasa katin #100 a layin ka na Airtel
- Sai ka danna wadannan code, *141*341*1#
- da zaran ka danna zasu cire #100 sai su baka data 120MB da minti 12 wanda zaka kira ko wane layi dashi.
Wannan tsarin yana da matukar kyau ga masu amfani da layin Airtel domin abubuwa guda biyu zaka samu a kan Naira 100 kachal
Datan da kudin kiran duk kwana 7 ne za suyi kafin su kare
Abu na farko da zaka samu shine data wato 120MB
Abu na biyu kuma shine lolacin magana na tsawon minti 12.
Wannan rubutun ya amfanar?
Yi sharing wa abokan ka dake social su ma su amfana da wannan tsari me sauki na Airtel.
Kana da tambaya?
Turo tambayar ka ta comment, zamu amsa maka a ko wane lokaci muna maraba daku
Mun gode