Labarai

SHIBA INU ya sake samun wani gagarumin nasara

SHIBA Burning

An sake kona SHIBA, SHIBA INU ya sake samun wani gagarumin nasara

An sake kona SHIBA INU guda biliyan 10 wanda yayi dai-dai da dalan amurka $123,000

Wani wallet da har yanzu ba a gano ko na waye ba ya kona SHIBA INU na dala 123,000 a yau 18/05/2022

Idan baku manta ba a farkon shekaran nan ne Team na SHIBA INU suka fitar da wani tsari na burning SHIB ga duk me bukatan yin hakan.

karanta

Sun ba da wannan daman ne saboda a samu daman rage yawan supply na token din domin a cilla darajan shi zuwa sama.

Sun samar da wani shafi ne wanda duk me bukata yayi burning din token din shi zai iya zuwa ya shiga kai tsaye yaje yayi.

Mutane sun fara yi tun a wancan lokacin sai dai wani abun mamaki ya faru a yau yayin da wani wanda ba a san ko wanene ba ya kona adadin shiba wuri na dukan wuri har miliyan 10.

Wannan labarin ya bada mamaki matuka ganin yawan kudin kuma ba a san ko waye ne yayi hakan ba.

Akwai kamfanoni da daidaikun mutane dama da suke karban SHIBA INU a matsayin kudin sayan kayan su.

Sannan kuma ga tsarin burning da suka fito dashi, sannan kuma mutane sun bada hadin kai domin a kai ga tudun na tsira.

Wannan token dai ya samu farin jini da daukaka kusan irin wanda ba a taba gani ba a duniyar meme token a lokacin da yake jariri.

KARANTA: Hanyoyin da za kabi ka koyi cryptocurrency

SHIBA INU ya sake samun wani gagarumin nasara

Kafin yanzu akwai wadanda suke ganin lallai SHIBA bazai kawo matsayin da yake a yanzu ba domin a wancan lokacin a na mishi kallon shitcoin ne.

Cikin kankanin lokaci ya bayar da mamakin da ba a taba zato ko tsammani ba.

Wani Karin ci gaba da SHIBA ya samu a wata daya zuwa biyu baya shine ya samu daman shiga babban kasuwan crypto wanda ake kira da robinhood.

Duk sunan wani Token ko Coin da zaka gani a wannan shafin ba cewa muke kaje ka saya ba a’ah labari kawai muke kawowa

Kasance damu a ko wane lokaci domin samun sabbin labarai game da cryptocurrency a harshen hausa

Turawa abokan ka

Mun gode

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button