Labarai

Exchanges 16 da suke son dawo da darajan LUNA

LUNA, UST stablecoin, LUNC

Exchanges 16 da suke son dawo da darajan LUNA, LUNA daya ne daga cikin cryptocurrencies masu girman daraja a kasuwan cryptocurrency a duniya baki daya

LUNA yana karkashin jagorancin Terra ne, kuma suna da stable coins mallakin kamfanin su mai suna UST.

Sai dai sun gamu da iftila’i yayin da darajan token din su ya karye yayi kasa fiye da tunanin me tunani

Ba a taba tsammani ko tunanin irin haka zai iya faruwa da LUNA ba saboda yadda suke da community mai karfi, Kwatsam sai gashi ya faru cikin kankanin lokaci

UST dama stable coin ne, farashin shi dai-dai yake da farshin dalar amurka, wato 1 UST = $1 amma sai da ya fado har kasa da $0.1

https://absanresource.com/2022/05/27/mace-ta-buge-maza-5-a-zaben-gwamnan-jahar-adamawa/

Abun nufi a nan shine darajan UST ya karye sai ya fado tun daga dala daya har zuwa kasa da $0.1

Wannan ne yasa shi ma LUNA ya samu matsala yayi ta saukowa kasa ba kakkautawa har sai da ya zama tamkar wani shitcoin saboda yanda ya zube kasa warwas

Kafin LUNA ya samu wannan matsalan ATH ya kai sama da dalan 119 ($119), da ya tashi rugujewa sai da ya koma kasa da $0.00008.

Terra LUNA zasu samar da sabon token

Bayan LUNA ya karye sai kamfanin suka cimma matsaya na samar da wani sabon LUNA yayin da za a chanjawa tsahon LUNA suna zuwa LUNC.

Yanzu haka an chanjawa tsohon LUNA suna zuwa LUNC, tuni dai wasu exchanges suka chanja kamar kucoin da sauran su.

AKIYAYE: duk coin da zamu ambaci sunan shi a wannan shafi, labari muke bayarwa, Absan Resource bai da alhakin duk wani asara da zaka iya samu a crypto.

Sabon LUNA zai shiga kasuwan crypto

sabon LUNA shine zai maye gurbin tsohon LUNA da ya karye

Tsohon LUNA zai kasance LUNC, sabon kuma LUNA.

Tuni dai exchanges na crypto da dama suka nuna goyon bayan su kan lamarin kuma suka tabbatar da cewa suna goyon bayan Terra LUNA kan wannan aiki na farfado da darajan LUNA.

Exchanges 16 da suke so su dawo da darajan LUNA

Daga cikin kasuwannin crypto da suka nuna goyon bayan su na dawo da darajan LUNA akwai wadannan;

 1. Binance
 2. KuCoin
 3. LBank
 4. Cryptocom
 5. FTX
 6. Bitfinex
 7. Kraken
 8. Huobi Global
 9. Bitrue
 10. Gateio
 11. Bitget
 12. MECX Global
 13. Bybit
 14. HitBTC
 15. Okcoin
 16. OKX

wadanan wasu ne daga cikin exchanges da suka nuna goyon su kan dawo da darajan LUNA a duniyar crypto.

Wannan rubutun ya amfanar?

turawa abokan ka domin su ma su amfana

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button