Cryptocurrency

Hanyoyin samun kudi a cryptocurrency guda 5

Hanyoyin samun kudi a cryptocurrency guda 5

Hanyoyin samun kudi a cryptocurrency guda 5

Hanyoyin samun kudi a cryptocurrency guda 5; Cryptocurrency yana da opportunities wato damanmaki masu yawa wadanda idan kayi amfani da wasu daga ciki zaka samu kudi a ko wace ranan duniya

ba zaka iya cryptocurrency ba dole sai ka karanta hanyoyin koyon cryptocurrency a saukake

Cryptocurrency harkoki ne da ya shafi kasuwancin coins, wadanda ake saya a sayar da nufin samun riba sai kuma abunda ba a rasa ba

A kasuwancin crypto zaka iya sa kudi kadan ka sayi token/coin idan kayi dace sai ya baka riba me yawa wanda baka taba tsammanin shi ba a dan karamin lokaci.

Wasu su suna ganin kamar a crypto da trading ne kadai ake samun kudi, toh batu na gaskiya ba haka bane domin hanoyin da ake samun kudi dasu a crypto baza su kirgu ba.

Crypto yana tafiya ne a kan tsarin blockchain, akwai opportunity masu yawa na samun kudi sai dai ko idan mutum bai yi bincike ba ko kuma bai sani ba.

Hanyoyin samun kudi a crypto guda biyar

Kamar yanda na fara bayani a farko, crypto yana da hanyoyi masu yawa da ake samun kudi a cikin shi sai dai kawai a yanzu zan baiyana wasu guda biyar ne daga cikin su.

Ga hanyoyin da zaka samu kudi dasu a crypto;

1. Crypto trading

Duk wani dan crypto yasan abun da ake kira trading a crypto domin kusan shine abu na farko da mafi yawan ‘yan crypto musamman sabbin suke faraway dashi.

Ko da yake wasu suna jahiltan kalman suna ganin cewa kawai ka sayi coin ka sayar shine trading, eyh tabbas shine trading amma ta yaya ake yin trading na cryptocurrencies?

Wannan itace tambayar da ba kowa ne yake iya amsawa ba saboda da yawa daga cikin mutane kawai suna neman ilimin saya da sayarwa ne sai suci gaba da sayan coin suna sayarwa

Idan kana son zama trader ya zama wajibi a gare ka da ka nemi ilimin Technical Analysis, kasan candles da chart pattern da sauran abubuwan dake da alaka dasu.

Idan ka iya technical analysis shine zaka iya fahimtan cewa coin sama zai yi ko kasa?

Da zaran ka kalli candles zaka iya fahimtan abunda ya faru a chan baya a kasuwa, ta hakan ne zaka iya sanin lokacin da z aka sayi coin da lokacin da zaka sayar.

Idan ka iya Technical Analysis za kasan menene support and resistance, wanda ya zama wajibi kayi aiki dashi matukar kana bukatan cin riba a kasuwa.

Akwai wasu trading din ma da a keyi ba tare da ilimin Technical Analysis ba, idan kayi nisa a crypto zaka fahimci hakan.

2. Buy and HODL

Buy and HODL yana nufin say aka rike

HODL appreviation ne, cikakken abunda yake nufi shine hold on for dear life, ana rubuta shine da manyan baki kamar haka HODL.

Rike coin na wani lokaci an fi samun alheri fiye da trading, wannan hanya ce da mutum zai sayi coin ko token ya rike shi na wani lokaci kafin ya sayar.

Holder yana iya rike coin na tsawon lokaci, wasu ma goge wallet din su suke yi sai su adana lambobin sirrin su sai bayan wani lokaci mai tsayi kafin su sake waiwayan wallet din su.

3. Staking

Staking na coin shima daya ne daga cikin hanyoyin da ake amfani dasu a crypto domin samun kudi.

Zaka iya sayan coin musamman don kayi staking din shi, yawan coin din ka zai na karuwa sannan kuma darajar sa tana sake karuwa.

Staking yana da tsare-tsare masu yawa, zaka iya staking coin kamar na shekara, watanni da sauran su.

Idan kayi staking coin din ka za ana kara maka yawan coin din, wannan yana matsayin kamar ladan staking da kayi ne.

Misali zaka iya sayan coin wanda za kayi holding din shi, maimakon ka ajiye shi kawai ta zaka iya staking din shi, yawan shi yana karuwa sannan kuma kana holding.

Wannan ya zama riba biyu kenan a gare ka.

4. Affiliate Programs

A crypto ma akwai tsarin affiliate marketing, shi ma hanya ne da zaka iya samun kudi me yawa sai dai kuma a tsarin affiliate idan kana da mutane za kafi samun kudi.

Yanda tsarin affiliate yake shine, exchanges na crypto da muke amfani dasu akwai wani guri na referrel program wanda idan ka wani yayi register ta link din ka na referrel zaka samu wani kaso na kudi zuwa wallet din  ka.

Wasu exchanges kuma sai suka masa suna da affiliate marketing, kusan ko wane exchange da irin tsarin ta na referrel program.

Wasu exchanges da zaran an yi register da link din ka zasu turo maka kudi a matsayin ladan ka shi kenan sai wani ya sake register da link din ka kafin su sake baka wani commission.

Akwai exchanges din da kuma za suci gaba da biyan ka duk lokacin da wanda yayi register da link din ka yayi trading wani coin ko token.

To ya kake gani idan ka samu Kaman mutane 100 su kayi ko mutum 30 ne su kaci gaba da amfani da wannan exchange zai iya yiwuwa kudin da zaka samu a wata yafi na wasu ma’aikatan gwamnatin.

5. youtube channel

Samar da youtube channel abu ne me sauki sai dai yana bukatan lokaci da sadaukarwa.

Idan ka iya crypto zaka iya bude youtube channel sai kaci gaba kirkiran video akan crypto kana dorawa a channel din n aka.

Idan kana yin abubuwan da mutane suke bukata zaka samu adadin subscribeers da watching hours da ake bukata

Idan ka kai wannan matakin adsense zasu fara dora talle a channel din sai suna biyan ka a wata.

Bayan nan kamfanonin crypto da daidaikun mutane zasu fara baka talle kana dorawa a channel suna biyan ka.

Hakan zai iya faruwa idan ka jajirce.

Wannan rubutu ya amfanar?

Turawa abokan ka domin su ma su amfana kuma su san hanyoyin da za su bi su samu kudi a kasuwancin sun a crypto

Kana da tambaya?

Idan kana da wata tambaya ko wani abunda baka gane ba, kayi comment ba da bata lokaci ba zamu baka amsa.

Disclaimer: bayanan da suka gabata a wannan rubutu ra’ayin marubucin ne sannan kuma ba financial advice bane, rubutu ne kawai wanda a ka yi shi domin ilimantarwa. kayi na ka binciken sannan ka nemi masu bada shawaran tattalin arziki kafin ka yanke hukuncin investing.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button