Coinmarketcap; Abubuwa 9 da ya kamata ka sani game dashi


Coinmarketcap; Abubuwa 9 da ya kamata ka sani game dashi
Coinmarketcap; Abubuwa 9 da ya kamata ka sani game dashi: Idan ka kai a kalla kwana daya da shigowa duniyan crypto abu ne mai matukar wahala a ce ba kaci karo da babban shafin nan na coinmarketcap ba.
Idan kuma hakan ta kasance, to a cikin wannan rubutu zan nuna maka yanda ake amfani da coinmarketcap da abubuwa guda tara da ya kamata ka sani a game da coinmarketcap
Coinmarketcap:
- Yana taimakawa domin sanin sabbin labarai dake da alaka da kasuwan cryptocurrency na duniya
- Yana dauke da bayanai na cryptocurrencies sama da dubbai
- Yana dauke da bayanan da ba sa cin karo da juna
- Coinmarketcap ya kasance daya daga cikin manyan websites guda dubu da ake dasu a duniya kamar yadda similarweb suka ruwaito
Na san ko a yanzu Ka fara fahimtan coinmarketcap.
Sai dai kuma wani abun mamaki ba ko wane dan crypto bane yasan yanda ake amfani da coinmarketcap, watakila ko saboda rashin kulawa ko wani dalilin na daban.
A wannan rubutu za kasan abubuwa da dama wadanda coinmarketcap ya kunsa, wadanda a ka fiye amfani dasu dama wadanda ba kowa ne yasan su ba.
Kaeanta: Hanyoyin samun kudi guda 5 a crypto
Abubuwa 9 da ya kamata ka sani game da coinmarketcap
Global Market Matrics
Fahimtar global market metrics shine abu na farko da ya kamata ka fara sani a yayin da kake koyon amfani da coinmarketcap.
Idan ka shiga coinmarketcap.com, a saman shafin za kaga ya kunshi wasu rubuce-rubuce masu yawa daga cikin su akwai wadannan;
- Yawan exchanges dake cikin coinmarketcap
- Yawan coins da suke kan coinmarketcap
- Total 24 hour volume
- marketcap
- Bitcoin dominance, da dai sauran su.
Wadannan wasu ne daga cikin abubuwan da global market metrics ya kunsa a coinmarketcap.
Accurate Coin Metrics
Idan ka taba kan ko wane coin a coinmarketcap, zai kai ka dashboard na wannan coin inda za kaga wasu abubuwa kamar haka;
- Farashin coin
- Trading volume
- Market capitalization (marketcap)
- Total, circulating da maximum supply na coin
Zaka iya research na ko wane cryptocurrency
Abunda ya kamata ka sani shine ba ko wane coin dake duniya bane a ka listing din shi a coinmarketcap, sai dai akwai dubbannin coin dake coinmarketcap.
Zaka iya binciken ko wane cointa hanyar rubuta sunan shi a akwatin bincike, zaka iya rubuta cikakken sunan coin misali Bitcoin, ko kuma da Ticker na coin misali BTC, da sauran su.
Graph dake dauke da bayanai na coins
Duk wani coin da ka taba shi zaka iya ganin graph wanda yake dauke da cikakken bayani wanda ya shafi coin din.
Ta hanyar amfani da graph zaka iya gane farashin da coin ya taba zuwa da kuma farashin da yake a daidai lokacin da kake dubawa.
Domin ganin graph na dake nuna tarihin farashin coin, a daidai lokacin da ka shiga dashboard na coin din sai ka dan gangara kasa kadan z aka gan shi.
A lokacin da kake duba graph, zaka iya yin wadannan;
- Ganin farashin coin a BTC, ETH da USD, ya danganci coin da kuma yanda kake bukatan ganin shi.
- Zaka iya chanja time frame na chart misali 1m, 1d 7d, 1y da sauran su, da sauran su.
Links masu muhimmanci na ko wane coin
Bayan ka taba kan coin ya kai ka dashboard, zaka iya ganin links masu muhimmanci game da coin (useful links).
Daga cikin wadannan links masu muhimmanci sun hada da;
- Website na coin
- Whitepaper
- Telegram
- Blockchain explorers
Wadannan links dake coinmarketcap amintattu ne, kuma suna da matukar muhimmanci musamman a lokacin da mutum yake yin fundamental analysis.
Manyan exchanges na crypto
Liquidity shine crypto, iya yawan liquidity da exchange yake dashi iya saukin saya da sayarwa da yake dashi.
Shiyasa wani lokaci za kaji ance an zarewa coin kaza liquidity, to a irin wannan yanayin babu halin sayar dashi ko da yana nuna farashi, zai kasance lambobi ne kawai marassa amfani.+
Zaka iya ganin best top exchanges da ake dasu na crypto a coinmarketcap.
Domin zuwa wannan shafin, ka koma home za kaga exchanges a can sama sai ka taba kai.
Bayanin akan crypto exchange
Bayan ka duba exchanges dake coinamrketcap, zaka iya taba kan daya domin kara sanin abubuwan da ya kunsa.
Zai kai ka dashboard na wannan exchange, a nan ma za kaga wasu links masu muhimmanci (useful links), kamar irin su;
- Shafukan sada zumunta na zamani na exchange
- Official website din su
- Sai kuma support, wato hanyoyin da za a iya tuntuban su idan bukatan hakan ta kama.
Sannan kuma zaka iya ganin duk trading pairs da ake amfani dasu a exchange.
Sanin inda zaka sayi coin
Ka ji sunan wani coin coin baka san inda zaka same shi ba?
Coinmarketcap zai taimaka maka wajen sanin exchange da coin yake.
Domin sanin exchange da zaka sayi coin, abun da za kayi shine;
- Kayi searching na sunan coin
- Ka taba market, za kaga sunayen exchanges da coin yake
- Ka duba farashin coin a ko wane exchange sai kaje ka saya a exchange da yam aka.
Sau da yawa za kaga mutane a group da dama suna tambayan wai a wane guri zasu samu coin su saya da haka ha rake damfaran wasu idan suka hadu da marassa gaskiya.
Note: kayi bincike ka tabbatar da ingancin exchange, sannan ka koyi yanda ake amfani da ita kafin kasa kudin ka a ciki.
Zaka iya kirkiran watchlist a coinamrketcap
Wani abun burgewa da coinmarketcap shine zaka iya kirkiran watchlist din ka a dan kankanin lokaci.
Zaka iya sa coins da kake bukatan bincike, saya ko ci gaba da sa musu ido a guri daya a coinmarketcap.
Domin sa coins a watchlist din ka, kaje dashvoard na coin sai ka taba kan alaman star wanda ke nuni da watch
Gainers da losers
Coinmarketcap yana bada daman ganin coins da suke haurawa sama da kuma wadanda suke gangarawa kasa a bangaren farashi.
Bana bada shawaran sayan coin wanda farashin shi ya riga ya haura sama, hakan yana iya jawo asaran da ba a shiryawa ba.
Disclaimer: bayanan da suka gabata a wannan rubutu ra’ayin marubucin ne sannan kuma ba financial advice bane, rubutu ne kawai wanda a ka yi shi domin ilimantarwa. kayi na ka binciken sannan ka nemi masu bada shawaran tattalin arziki kafin ka yanke hukuncin investing.