Cryptocurrency

Hanyoyi 4 da ake samun kyautan cryptocurrencies

Hanyoyi 4 da ake samun kyautan cryptocurrencies

Hanyoyi 4 da ake samun kyautan cryptocurrencies, Ana samun Karin yawaitan masu shigowa crypto kuma kusan kullum ana samar da sabbin coins.

Akwai kamfanoni da dama da a yanzu suke karban cryptocurrencies a matsayin kudi

Sannan akwai platforms da dama da suke bada dama mutum yayi amfani da cryptocurrencies dake wallet maimakon cire kudin dake cikin aljihun ka.

Wannan da ma wasu dalilai da ban kawo su ba a nan ya haddasa hanyoyin mallakan crypto yayi sauki, ba tare da ka kashe kudi ba zaka iya samu a kyauta idan kabi hanyar data dace.

Wannan rubutu zai yi cikakken bayani ne a kan yanda zaka samu kyautan crypto, zan baiyana 4 daga ciki a yanzu.

kyautan cryptocurrencies, yanda ake samu cikin sauki

Idan ka sa kudin ka a crypto har ka samu daman sayan coins ka ajiye a wallet ko exchange din ka na crypto.

Zaka iya fahimtan cewa farashin coin yana iya hawa da sauka a ko wane irin lokaci.

Saboda haka  abu ne me muhimmanci a gare ka da ka nemi Karin wasu hanyoyin da zaka samu crypto a kyauta, ko da farashin ya karye bazai daga maka hankali ba

Sannan kuma zaka iya sayarwa a ko wane lokaci matukar dai akwai daman sayarwan tunda ba kudi kasa kasa mas aba.

  1. Staking
  2. Airdrop
  3. Kammala course
  4. Mining

Wasu hanyoyin kuma da ake samun kyautan crypto sun hada exchanges na crypto, misali idan ka shiga nan kayi register da babban kasuwan Cryptocurrency na OKX za kana samun kyautan crypto da zaran wani yayi register ta referrel link din ka.

Hanyoyin da ake samun kyautan crypto suna da yawa sosai sai dai kawai mutum yasan wanda ya sani ko kuma ya dauki wanda yafi gamsuwa dashi.

Guda 4 da na baiyana a sama kadai ne zan yi bayani a kan su;

Staking 

Domin samun kyautan crypto a ko wane rana zaka iya staking wani coin da kake dashi sai suna baka ladan staking da coin din da kayi staking.

Zaka duba coin dake kan tsarin POS wato proof of stake sai ka saya ka ajiye shi a exchange sai kayi staking

Za kana samun coin din ne bisa ga adadin coin da kayi staking.

Airdrop

Abu na biyu shine airdrop, akwai airdrop da dama da ake yi kuma ana samun alkhairi a wasu.

Sai dai yana da muhimmanci kayi bincike ka tabbatar da ingancin airdrop kafin kayi domin akwai wadanda ban a gaskiya bane.

Hatta coins da suke da exchanges na su na karan kan su wasu lokutan suna yin airdrop, sannan kuma wasu tokens din ana airdrop din su ne a lokacin da suke presale.

Airdrop yana zuwa ta hanyoyi da dama, akwai wadanda a yanzu suke da jari me yawa a crypto kuma a dalilin airdrop ne suka samu.

Akwai wadanda basa yin airdrop saboda tunanin mafi yawa wahala kawai ake sha daga karshe baza ka sake jin labarin token din ba.

Eyh tabbas hakane amma ana samun na gaskiya wadanda ake samun alheri me yawa dasu, tunda ba kudi zaka kashe ba gara kayi idan tayi kyau zaka murmusa.

karanta:

 Telegram 10 da suke bada accurate signal domin trading

Hanyoyi biyar da ake samun kudi a crypto

Kammala course

Wannan ma wata dam ace da ake samun crypto a kyauta bayan mutum ya kammala karanta wani course.

Wannan yana faruwa ne ta hanyar karatu, kallon videos na wani course sai ana baka kyautan wani token na crypto.

Daga cikin manyan platforms da suka shahara a wannan bangaren akwai coinbase, daya ne daga cikin manyan kasuwannin crypto a duniya.

Coinbase suna bada kyautan ne bayan kayi karatu, kallon videos da amsa tambayoyi (quiz).

Mining

Mining shi ma daya ne daga cikin manyan hanyoyin da ake samun kyautan coins dashi.

Mining yana da lokacin da ake yin sa, sai dai da yawa ana yi ne duk bayan awa 24.

Bayan ka sauke application na mining, wani guri kawai zaka taba sai ya fara reading nan take za kaga sun baka kyautan crypto, bayan awa 24 sai ka sake tabawa.

Yanazu haka dai mining da a keyi wanda masana crypto suka tabbatar da ingancin sa shine RENEC, coin ne babban kasuwan crypto na duniya me suna Remitano.

Remitano kasuwa ce da take da blockchain din ta, sannan an fara samar da ita kafin daga baya aka samar da binance, yanzu ne suka samar da coin kuma ta hanyar mining kadai ake samun shi.

Duk da an kusa launching amma har a yanzu zaka iya amfani da wannan daman ka far aka tara ko kadan ne zuwa lokacin da za ayi launching mu sha jar miya.

Shiga nan kayi register da verification zuwa level 2 domin fara mining RENEC coin.

Disclaimer: bayanan da suka gabata a wannan rubutu ra’ayin marubucin ne sannan kuma ba financial advice bane, rubutu ne kawai wanda a ka yi shi domin ilimantarwa. kayi na ka binciken sannan ka nemi masu bada shawaran tattalin arziki kafin ka yanke hukuncin investing.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button