Cryptocurrency

koyon Crypto; Youtube channels 5 da zaka koyi Cryptocurrency

koyon Crypto; Youtube channels 5 da zaka koyi Cryptocurrency

shin kana so ka fara koyon cryptocurrency amma kuma ba kasan ta ina zaka fara ba?

Cryptocurrency kasuwanci ne wanda dole sai an koye shi kafin za a iya har a samu kwarewa a fara koyawa wasu masu bukatan koyo.

koyon Crypto; Youtube channels 5 da zaka koyi Cryptocurrency
koyon Crypto; Youtube channels 5 da zaka koyi Cryptocurrency

youtube jami’a ce ta musamman domin babu wani ilimin da zaka nema wanda za a rasa shi sai dai ko idan watakila binciken ka yayi karanci.

kamar yadda ake da telegram channel masu bada signal na crypto haka ma akwai youtube channels masu yawa wadanda suke koyar da cryptocurrency tun daga matakin faraway har zuwa kwarewa.

Ganin cewa crypto baya yiwuwa sai da ilimi hakan yasa mutanen da suke kwarewa a wani fannin ilimin crypto suke bude channel suna koyarwa a kyauta.

Wasu channel din technical analysis suke koyarwa kadai, wasu kuma fundamental analysis suke koyarwa, wasu trading suke koyarwa, wasu bangaren NFTs su kafi bada karfi.

Wasu kuma sun hada duk wani ilimin dake alaka da crypto ne suke koyarwa, da dai sauran su.

koyon Crypto; Youtube channels 5 da zaka koyi Cryptocurrency

Cikin wannan rubutu zan baiyana wasu youtube channel biyar da suke koyar da crypto, idan kana bibiyan su zaka samu ilimin crypto idan ka mai da hankali kan koyo.

Idan ka koyi crypto zaka budewa kan kan ka wasu hanyoyin samun kudi wadanda baka taba zato ko tsammani ba.

Bitboy Crypto

BitBoy Crypto daya ne daga cikin manyan channel na youtube da suke dora video da suka shafin kasuwan cryptocurrency.

BitBoy Crypto channel ne da yake kara samun daukaka da sanuwa a duniya ta hanyar dora videos na interviews da sabbin labarai na crypto.

Ba a nan kadai ya tsaya ba, tsokaci a kan projects daban-daban da kuma bada shawarwarin yanda ake trading cryptocurrency.

 

Hanyoyi 4 da ake samun kyautan cryptocurrencies

 

Coin Bureau

Coin Bureau daya ne daga cikin channel na duniya da suke wayar da kan al’umma a kan kasuwan cryptocurrency da forex.

Team din su suna yin analysis na cryptocurrencies da forex trading.

Coin Bureau basu dora talla (Ads.) ba a channel din su saboda babban burin su shine su dora quality content.

The Moon

Carl the moon yana dora video na technical analysis, farashin cryptocurrencies da labaran da suka shafi kasuwan cryptocurrency a duniya.

Carl yana Magana a kan hatsarin dake cikin swing da leverage trading a kasuwan cryptocurrency.

Altcoin Daily

Altcoin daily suna matukar kokari wajen dora videos na labarai, ilimi da market analysis a channel din su na youtube.

Altcoin daily suna da subscibers sama da miliyan daya a channel din su.

Jacob crypto bury

Idan kai dan koyo ne ko kuma yanzu ne kake son fara neman ilimin crypto, wannan channel din ne ya kamace ka.

Wannan channel daga cikin aikin da su keyi akwai neman projects masu marketcap kadan (small marketcap), NFTs, sannan kuma suna hasashen farashin coins (price prediction).

Kullum yana sake update na abunda yake tafiya a kasuwan crypto a saukakakken harshe.

 

Disclaimer: bayanan da suka gabata a wannan rubutu ra’ayin marubucin ne sannan kuma ba financial advice bane, rubutu ne kawai wanda a ka yi shi domin ilimantarwa. kayi na ka binciken sannan ka nemi masu bada shawaran tattalin arziki kafin ka yanke hukuncin investing.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button