Cryptocurrency

Farashin Bitcoin da Altcoins a yau, me ya kamata kayi?

Farashin Bitcoin da Altcoins a yau, me ya kamata kayi?

A dai-dai wannan lokaci zamu tattauna ne a kan yayin yadda kasuwan crypto take tafiya musamman a bangaren farashi.

Duk wanda yake crypto a yanzu yasan yanayin da ake ciki na bear market, wanda zamu iya cewa kusan ko ma fiye da shekara kenan ake ciki.

Sai dai kasuwan ta dan fara dagawa na wasu ‘yan kwanaki ko awannai ba tare da zato ko tsammani ba sai a sake komawa gidan gidan jiya.

Farashin BTC yayi kasa sosai, haka ma sauran coins wadanda a ke yiwa lakabi da Alrcoin duk sun yi kasa sosai.

A wannan lokaci saboda yanayin da a ka shiga na DIP har wasu musamman sabbin shiga suke ganin kamar ko dai damfara ce?

karanta:

Batu na gaskiya babu wata damfara kai dai kawai yanayin yanda a ka sako kasuwan a gaba ne tun daga kan SEC har zuwa whales da suke jujjuya kasuwan ta yanda suka ga dama.

Whales sune masu kudin crypto, duk coin da suka saya zai farashin shi zai yi sama saboda irin kudin da suke zubawa.

Haka kuma idan suka sayar nan ma farashin coin zai yi kasa, babban abunda za kayi shine neman ilimin crypto da sanin coins masu inganci da zaka saya

Idan coin masu inganci ka saya ko da DIP ya zabtare farashin su, da zaran kasuwa ta murmure kudin ka zai dawo har da riba.

Farashin Bitcoin da Altcoins a yau, me ya kamata kayi?

Farashin Bitcoin da Altcoins a yau, me ya kamata kayi
Farashin Bitcoin da Altcoins a yau, me ya kamata kayi

Ga farashin BTC a yau;

  • BTC $23800

Farashin Altcoin a yau

Ga farashin wasu daga cikin Altcoin;

  • ETH $1190
  • BNB $221
  • OKB $10.3
  • KCS $ 11.45
  • MATIC $0.4
  • XRP $0.3

sauran coins suma dai sun ji jiki kuma suna ci gaba daji har yanzu

Ya za ta kasance idan ka samu coins masu kyau ka fara DCA daga yanzu zuwa lokacin da kasuwa zata dan dago? NFA, DYOR

Wannan dai shine Farashin Bitcoin da Altcoins a yau da abun da ya kamata me kayi

kuyi subscribe na News letter domin samun sabbin rubuce-rubucen mu ta Email.

 

Disclaimer: bayanan da suka gabata a wannan rubutu ra’ayin marubucin ne sannan kuma ba financial advice bane, rubutu ne kawai wanda a ka yi shi domin ilimantarwa. kayi na ka binciken sannan ka nemi masu bada shawaran tattalin arziki kafin ka yanke hukuncin investing.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button