Cryptocurrency

kasan hatsarin dake cikin crypto kafin sa kudi

kasan hatsarin dake cikin crypto kafin sa kudi, Kusan ko wane irin harkalla da ya shafi shige da ficen kudi akwai hatsari da ake iya fuskanta, haka ma crypto akwai hatsarurruka da zaka iya fuskanta musamman idan ka fara sa kudi ba tare da neman ilimi ba.

Babban hatsarin da zaka iya fuskanta shine rasa kudin ka, kamar abun da ya faru da $LUNA kwanan nan, mutane da dama sun rasa dukiyar su, wasu ma ance sun rasa ran su.

Fara neman ilimin crypto kafin sa kudi shine abu mafi dacewa a gare ka kai da kake bukatan fara kasuwancin cryptocurrencies.

Sai dai kuma duk ilimin ka akwai abunda zai iya faruwa da project wanda zai iya jefa ka cikin asara, kar hakan yasa kace zaka yanki durum ka shiga tunda abun sa’a ne kawai.

Ilimi farko, sa kudi ya biyo baya, daga nan kuma sai kirga riba.

crypto
kasan hatsarin dake cikin crypto kafin sa kudi

kasan hatsarin dake cikin crypto kafin sa kudi

1. Idan kai ba me iya daukan babban kasada bane zaka iya trading manyan coins kadai kamar irin su bitcoin, etherium da Binance coin.

2. Idan kuma zaka iya daukan ko wace irin kasada zaka iya bincika wasu coins sai ka duba wanda kake gani za ka iya trading dashi.

sai dai kuma an fi samun alkhairi a kananan projects, misali idan kayi sa’a zaka iya samun X10 ko sama da haka a kankanin lokaci.

kamar BTC, nawa za kasa ya maka ko da X2 ne? 🤔

kayi iya yin ka domin kare dukiyar ka saboda gara ace baka samu riba ba daka rasa kudin ka.

Zaka iya amfani da coinmarketcap domin samun wasu projects.

Disclaimer: bayanan dake wannan shafin ra’ayin marubucin ne sannan kuma ba financial advice bane, rubutu ne kawai wanda a ka yi shi domin ilimantarwa. kayi na ka binciken sannan ka nemi masu bada shawaran tattalin arziki kafin ka yanke hukuncin investing.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button