Menene Dollar Cost Averaging (D.C.A)

Menene Dollar Cost Averaging (D.C.A)
kana cikin bincike domin gano menene Dollar Cost Averaging da muhimmancun sa da kuma yanda ake amfani dashi a yayin sayen cryptocurrency?
toh barka da zuwa a dai-dai wannan lokaci ka samu abunda kake nema, zamu faiyace bayani a kan ma’anar DCA da yanda za kayi amfani dashi.
kafin kasan akwai hanyoyin da za kabi ka koyi cryptocurrency cikin sauki?

Dollar cost average wata hanya ce da mutane suke amfani da ita domin sayan crypto, Dollar cost average Yana nufin sayan crypto da kadan-kadan daga lokaci zuwa lokaci, da haka har mutum ya tara crypto mai yawa.
Idan kana da dala dari biyu ($200) sai ya kasance kana bukata zaka sayi wani project to idan za kayi amfani da DCA ne baza ka zuba $200 a lokaci daya ba.
Misali zaka iya farawa da sayan kamar na $100, bayan wani lokaci kasa kamar $50 ko kasa da haka, haka za kaci gaba dayi har zuwa lokacin da kudin daka tanada don sayan project din ya kare.
Ana samun alheri sosai ta wannan hanya idan za kayi trading musamman a lokacin da farashin coin yake yin kasa, da zaran ya fara tasowa zai iya fitar maka da kudin ta tare da riba ko da motsi kadan yayi.
Idan riba kake bukata sosai a crypto yana da muhimmanci ka fara amfani da Dollar cost average a duk lokacin da zaka sayi crypto.
MUHIMMANCIN DOLLAR COST AVERAGE
Dollar Cost Average yana da amfani sosai a crypto, daga ciki su akwai:
• Samun riba me yawa; a yayin da kake trading cryptocurrencies ta hanyar amfani da DCA zaka iya samun riba me yawa da zaran farashin coin ko token da ka saya ya fara motsawa sama
Missali zaka iya sayan coin na dala hamsin ($50) a kan $0.5 ko wane guda daya, sai farashin shi ya sake yin kasa zuwa $0.4 ko kasa da haka.
A wannan lokacin sai ka sake zuba masa kamar dala hamsin ($50), idan farashin coin din ya fara tasowa sama yazo kamar farashin shi na $0.5 zaka kasance ne cikin riba a dalilin amfani da DCA da kayi.
Da a ce ka saka dala darin ($100) lokaci daya ne sai farashin token din ya haura $0.5 kafin zaka fara kirga riba amma da yake kayi amfani da DCA tun kafin farashi yazo $0.5 zaka fara kirga riba.
• Zuba kudi mai yawa ba tare da ka jijjiga ba; a lokacin da kake DCA zaka iya sa kudi me yawa a crypto ba tare da kaji jiki ba.
• Tara adadin coin me yawa; zaka iya mallakan token mai yawa ta hanyar DCA kafin ka ankara.
Misali zaka iya cewa duk sati zaka sayi token kaza daga cikin riban da kake samu a trading, da haka zaka iya tara wani token me yawa har ya baka riban da ba kayi tsammani ba.
Disclaimer: bayanan dake wannan shafin ra’ayin marubucin ne sannan kuma ba financial advice bane, rubutu ne kawai wanda a ka yi shi domin ilimantarwa. kayi na ka binciken sannan ka nemi masu bada shawaran tattalin arziki kafin ka yanke hukuncin investing.