Cryptocurrency

manyan masana crypto 5 daza kayi following a twitter

Manyan masana crypto 5 daza kayi following a twitter; Idan labari kake nema game da abubuwan suke faruwa a kasuwan Cryptocurrency babu inda yafi dacewa kamar twitter.

Wannan ne babban dalilin da yasa muka tsamo manyan shafukan masana Cryptocurrency guda biyar a twitter da ya kamata kana bibiyan su a ko wane lokaci

Kasuwan Cryptocurrency tana hawa da sauka a ko wane lokaci, hakan yasa dole mai yin kasuwancin yayi taka tsantsan.

Rashin yin taka tsantsan a crypto yana iya jefa mutum cikin hatsari da fargaban yin asaran da zai iya bijirowa a ko wane lokaci.

Babban hikima da dabaran da za kayi a matsayin ka na dan crypto shine bibiyan mutanen dake sama da kai a ilimin Cryptocurrency.

Ta hakan ne zaka fahimci yanda tsarin kasuwan take tafiya dare rana, safe da yamma.

Wadannan mutane suna sake update a kan abubuwan dake tafiya a kauwan crypto, bibiyan su a ko wane lokaci zai sa ka fahimci yanayin da kasuwa zata iya kasance wa a nan gaba.

Magana daya tana iya sauya yanayin yanda kasuwan crypto yake tafiya, misali daga sama zuwa ƙasa ko daga ƙasa zuwa sama.

Idan a ka samu wani labari me dadi wanda ya danganci kasuwa sai kaga farashin coins sun yi sama

Haka mumunan labari ke juya yanayin tafiyan kasuwan Cryptocurrency daga sama zuwa ƙasa.

KARANTA: Yanda zaka gane coins da manyan whales suke saya

crypto
crypto

manyan masana crypto 5 daza kayi following a twitter

Elon Musk

Wannan sune jerin sunayen manyan masana ilimin Cryptocurrency 5 da ya kamata kayi following a twitter;

Ko ba a yi wani bayani ba a kan Elon Musk ba laifi bane domin ina da tabbacin kana jin sunan shi matuƙar kana bibiyan al’amuran yau da kullum.

Elon Musk shine yafi kowa kuɗi a duniya yanzu haka, ya samu ƙudi me tarin yawa a crypto sannan yana da kamfanoni da dama.

Yana da ƙarfin da idan ya rubuta sunan coin ko token Nan take za kaga farashin sa ya fara yin sama, mutane saya suke ido a rufe shiyasa yake sama.

Musk Yana da mabiya sama da miliyan 100 a twitter kuma mafi yawa daga cikin su ‘yan Crypto ne.

CZ Binance

Da wahala ka samu ɗan crypto wanda bai san CZ ba, yana da mabiya kusan miliyan shida a twitter.

CZ shine mamallakin babban kasuwan Crypto (Exchange) na ɗaya a duniya wato Binance, abun farin ciki ne gare ka kana bibiyan shi a twitter a matsayin ka na ɗan crypto.

Watcher Guru

Watcher guru shafi ne a twitter wanda yake faiyace bayani da labarai wanda suka shafi Cryptocurrency.

Ko wane rana yana sake labarai na kasuwan Cryptocurrency a shafin shi musamman ɓangaren NFTs da Cryptocurrency.

Crypto Rover

Crypto Rover daya ne daga cikin manyan masana ilimin Crypto wanda yake bayani da ɗora videos da bayanin yanayin da kasuwa zata iya tsintan kan ta a ciki.

Shafin Crypto Rover ya fi mayar da hankali ne a ɓangaren Technical Analysis na Cryptocurrencies, ko wane lokaci yana ɗora videos masu matuƙar muhimmanci ga ‘yan crypto.

The Moon Carl

The MoonCarl shima dai ya shahara a ɓangaren crypto kuma yana sake sabbin labarai game da Crypto.

Zai taimaka sosai idan kana bibiyan shi domin zaka samun ƙarin tarun ilimin Crypto da yaddan Allah.

Muhimmancin following manyan masana Cryptocurrency a Twitter

  1. Za kasan duk abubuwan da zasu iya faruwa a kasuwan crypto: 

manyan masana crypto dazan baiyana su a suna rubuce-rubuce a kan crypto ko wane lokaci.

Wannan ne zai sa ka kasance cikin sanin shige da ficen kasuwan, wani abun za ka sani tun kafin ma ya faru a kasuwa.

  1. Sanin lokacin da zaka sayar da coin:

Zaka iya sanin lokacin da zaka sayar da coin ɗin ka saboda wasu labarai da za kaji wanda zai iya sawa kasuwan ta jijjiga ko ma a shiga DIP.

  1. Sanin lokacin da zaka sayi coins:

Ganin cewa wasu kuma sun fi mai da hankali ne a bangaren technical analysis, suna daukan coin daban-daban suna analysis a Kai

Wannan zai baka daman sayan coin a lokacin da ka samu ƙofan shiga, sannan kuma ka fita a daidai lokacin da ya dace.

Ta wannan hanyar za kana samun riba me gwaɓi a kasuwan crypto ta yanda watakila baka taɓa tsammani ba.

Disclaimer: bayanan dake wannan shafin ra’ayin marubucin ne sannan kuma ba financial advice bane, rubutu ne kawai wanda a ka yi shi domin ilimantarwa. kayi na ka binciken sannan ka nemi masu bada shawaran tattalin arziki kafin ka yanke hukuncin investing.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button