Cryptocurrency

Yanda zaka gane coins da manyan whales suke saya

Yanda zaka gane coins da manyan whales suke saya; Wasu dai-daikun mutane ko kamfanoni suna da matukar karfi fiye da kowa, wadannan su ake kira da whales a crypto.

A cikin wannan rubutun zaka fahimci irin coins da whales suke saya, lokacin da suke saya da duk wani motsin su a kasuwar crypto.

Mutane da dama suna tabka asara a crypto musamman sabbin shiga saboda da yawan su basu san ta ina zasu far aba, basu san abun da ya dace suyi ba, wannan yake sa da yawan mutane suke tabka asara a kasuwan cryptocurrency.

Whales sune manyan masu kudi a crypto, idan ka fahimci coins da suke shiga kan ka zai kara wayewa kuma zaka iya shiga da zaran ya baka riba sai ka fita.

Su Wanene whales a crypto?

Whale shine wani mutum ko wata kungiya da take rike da kaso mai yawa na cryptocurrencies.

Whale da ya sayi wani kaso mai yawa na crypto yana iya juya kasuwan a zuwa sama, a yayin da ya sayar kuma kasuwar za ta iya yin kasa.

Babu wani takamammen yawan token ko coin da mutum zai rike a kira shi da whale, amma duk wanda yake rike da Bitcoin guda dubu daya (1000 BTC) ana kiran shi da suna whale.

Sai dai kuma abun ba haka yake ba a bangaren altcoin, adadin yana sama sosai da 1000 saboda market caps na alcoin yana kasa sosai dana Bitcoin.

Yanda zaka gane asset da whales suke saya

Bari na dan yi maka bayani a takaice a kan yanda zaka gane asset whales suke saya, da yake cryptocurrency yana kan tsarin blockchain ne za a iya tracking coins da whales suke saya.

Idan zaka duba tokes da whales suke saya, zaka duba wallet ne da yake dauke da adadin BTC (Bitcoin) a kalla guda 1,000.

Akwai hanyoyi da dama da zaka fahimci shige da ficen whales a kasuwan crypto, daga ciki akwai shige da ficen coins daga wani guri zuwa wani guri kamar;

  • daga exchange zuwa wallet
  • daga wallet zuwa exchange
  • wallet zuwa wallet

Ta wannan zirga-zirga da a keyi da coins zaka fahimci asusun ajiyan da yake dauke da a kalla bitcoin 1,000, duk inda ka gani kai tsaye ka kira shi da whale, da fatan dai ka fahimci wanene whale a yanzu?

KARANTA: Hanyoyi 4 da zaka samu kyautan crypto

Whales basa doguwar ajiya (long term HODL) a exchange, shiyasa mafi yawa idan sun saya a exchange za kaga sun tura shi zuwa wallet, idan kuma zasu sayar sais u turo daga wallet zuwa exchange.

  • Blockchain explorers

Blockchain explorers shima yana taimakawa wajen gane transactions da a keyi a kasuwan crypto, domin za kaga har yawan tokens ko coins da mutum yake rike dashi, ta hakan zaka iya gane whales.

Yanda zaka gane coins da manyan whales suke saya
Yanda zaka gane coins da manyan whales suke saya

Yanda zaka gane coins da manyan whales suke saya

Bayan wadanda muka baiyana a sama, ga wasu hanyoyi 5 da ake gane coins da manyan whales suke saya;

Idan kana amfani da wadannan hanyoyin zaka fahimci yanda crypto yake a zahirance, kuma za kafi kwarewa fiye da yanda kake a yanzu.

Da fatan ka amfana? kayi sharing zuwa ga ‘yan uwa da abokan arziki domin su amfana kamar yanda kai ma ka amfana. mun gode

Disclaimer: bayanan dake wannan shafin ra’ayin marubucin ne sannan kuma ba financial advice bane, rubutu ne kawai wanda a ka yi shi domin ilimantarwa. kayi na ka binciken sannan ka nemi masu bada shawaran tattalin arziki kafin ka yanke hukuncin investing.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button