Cryptocurrency

Ma’anar Fundamental Analysis a cryptocurrency

Ma’anar Fundamental Analysis a cryptocurrency; Shin kai dan crypto ne amma ba kasan menene fundamental analysis ba? kana ta bincike kwatsam sai kaci karo da wannan rubutun, tabbas a yanzu za ka fahimci abun da fundamental analysis yake nufi a crypto.

Muna da project masu yawa na crypto kuma kullum cikin kirkiran sabbi ake, babban kalubalen da ake samu shine akwai na ‘yan damfara, wani coin ko token din tun kafin a gama presale suke guduwa bayan sun cimma burin su.

Wasu kuma zasu kammala presale amma baza su sa shi a kasuwa ba sai dai suyi ta yaudaran wadanda suka zuba kudin su suka saya, Wasu kuma zasu shiga kasuwa sai dai ba masu dauwama bane ko ba dade ko ba jima zaka neme su ka rasa.

Akwai misalai a kan wannan shimfida da nayi sai dai gudun kace-nace bazan ambaci sunan token ko daya ba, idan ka kai shekara a harkan crypto zai yiwu ka ci karo da ire-iren su.

Ma’anar Fundamental Analysis a cryptocurrency

Hanyoyin da ake bi a gane cewa wannan coin ko kuma project mai inganci ne ko dai an gina shine saboda a cuci mutane, wannan binciken shi ake kira fundamental analysis.

MENENE FUNDAMENTAL ANALYSIS?

Fundamental analysis ya kunshi bincike ne da tattaro bayanai da suka shafi wani project domin gano inganci ko rashin ingancin sa, misali za a iya binciko amfani ko dalilin kirkiran shi, team da suka kirkira, wasu alkawura suka dauka a baya sannan sun samu daman cikawa ko dai kullum waina hankalin jama’a suke?, yawan adadin coin/token da sauran su.

Bayan an kammala wannan bincike sai a samar da matsaya akai na ya dace a saya ko dai kar a saya saboda wani nakasu da ake gani kamar ya samu bisa sakamakon binciken da a kayi.

Wani zai iya bincike ya gano cewa coin yana da inganci, kai kuma watakila sakamakon binciken ka zai iya nuna maka rashin inganci to me ya dace kayi idan irin haka ta kasance?

Shawaran da zan baka anan shine matukar ka ga matsala komai kankantar ta ga project to ka rabu da ita kawai, ta yiwu wancan bai hango abunda ka hanga bane.

KOWA DA TSARIN SHI NA FUNDAMENTAL ANLYSIS

  • Wani idan yaga total supply na coin yayi yawa baya ma bata lokacin shi da sunan bincike a kai
  • wani da zaran ya ga white paper bai kwanta masa a rai ba, baya ci gaba da bincike daga nan yake yanke hukunci
  • wani kuma team yake fara dubawa idan ya bibiyi tarihin su yaga daga ciki akwai wani me mumunan tarihi ko wani abu na rashin gaskiya a tattare dashi, daga nan yake dakatar da bincike
  • wani kuma tsarin raba coin yake dubawa ya ga ko wane bangare kashi nawa a ka ware musu.
  • Wani kuma sai ya kammala bincike ya tattaro duk wasu nakasu da project din yake dashi domin ya samu cikakkiyar gamsuwa da sakamakon binciken sa.

Abunda yasa na kawo wadannan misalai shine yana da kyau duk abun da za kayi ka kasance da dalili, kar ka gama bincike wani ya tambaye ka ingancin coin kace masa a binciken ka bai da inganci, idan ya tambaye ka dalili ka rasa abunda za kace masa, kuma duk abunda ya shafi bada shawara a kan crypto ka sanar da mutum cewa yaje yayi na shi binciken.

Idan ka bada shawara wa mutum ya sayi wani coin sai a ka samu akasi darajan coin din ya karye wani zai iya yawo da sunan ka da sunan ka cuce shi ko wani abu me kama da haka.

wannan ne dalilin da yasa za kaga har manyan ‘yan crypto suna cewa ‘Not Financial Advise’ (NFA), ‘Do Your Own Research’ (DYOR), ma’ana ka sanar da mutum cewa kai ba shawaran tattalin arziki ka bashi ba sannan kuma yaje yayi na shi binciken.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button