Altcoins a cryptocurrency cikakken bayani da abubuwan da ya kunsa

Altcoins a cryptocurrency cikakken bayani da abubuwan da ya kunsa; A cryptocurrency akwai bitcoin da altcoins, a wannan rubutu zamu tattauna sannan muyi cikakken bayani a kan altcoin, yanda zaka fahimce shi yadda ya kamata.
A matsayin ka na dan crypto, ko da a ce baka wuce sati daya da farawa ba da yiwuwan ka taba jin wannan kalma ta ‘Altcoin’
Idan ba kasan me altcoin yake nufi ba, ko kuma ka sani amma kana kokwanto haka ne ko ba haka ba, yanzu duk wannan kuran za ta kau bayan ka kammala karanta wannan rubutu.
Altcoins a cryptocurrency cikakken bayani da abubuwan da ya kunsa
Menene altcoin a cryptocurrency
Idan kaji ance Altcoin ana nufin duk wani coin wanda ba Bitcoin ba, bitcoin ne coin na farko da a kaci nasaran samarwa a duniyan cryptocurrency.
Bayan Bitcoin akwai wasu dubban coins da aka samar kuma ake kan samarwa har zuwa yanzu, toh wadannan coins da kake gani bayan bitcoin sune alt coins.
Zaka iya cewa altcoins ko kuma alternative coins, duk yadda ka kira dai-dai ne.
Rabe-raben alt coins a cryptocurrency
A yanzu haka a crypto muna da coins guda dubu ashirin da dari uku da chasa’in da tara (20, 399) kamar yadda babban shafin coinmarket cap ya baiyana.
Bitcoin shine yake dauke da kusan rabi na marketcap na kasuwan cryptocurrency, Etherium yake biye masa sai sauran altcoins suke dauke da sauran Kason.

Ga wasu daga cikin alt coins;
- Etherium
- BNB
Uniswap
- Cardano
- Dogecoin
- Chainlink
- Solana
- LUNA
- KCS
- OKB
Za ka iya sayan altcoins?
Akwai hatsari a cikin sa kudi a crypto domin farashin coin yana iya juyawa a ko wane irin lokaci, hakan ne yasa nake bada shawara kafin ka sayi coin ka tabbatar kayi bincike kasan ingancin shi.
Kar ka sayi coin don ka ga sunan shi a shafukan sada zumunta ko cikin abokai, yin haka zai iya jefa ka a asara.
Ko fundamental analysis kadai ka iya za kaci kasuwan crypto, koyo shine gaba da sa kudi kuma ilimi da hakuri ne babban jari a crypto.
Fundamental analysis yana baka daman iya bincike da tantance ingancin coin, to kaga wannan ba karamin ilimi bane domin har signal zaka iya bayarwa ana biyan ka
Sannan idan ka kware akwai wadanda zasu iya baka coins kayi musu bincike a kai sais u biya ka ladan aiki ka, akwai damanmaki da yawa a crypto da zaka samu kudi, amma sai ka daure ka koya.
Kar ka dauka cewa crypto hanya ce da ake samun kudi da gaggawa, a’ah sai ka nemi ilimi sannan kayi aiki tukuru kafin ka fara samun kudi.
Ba altcoin kadai ba, hatta Bitcoin ba lallai ne ka iya cin riba a kan shi ba da gaggawa, zaka iya sa kudi sai farashin shi yayi kasa.
Sai ya kasance idan ka sayar a wannan lokacin asara za kayi, amma da za ka hakura zuwa wani lokaci sai ka sayar a riba.
Altcoins sun zo ne don su tabbata?
Wannan amsar mai sauki ne amma kuma yana da wahala, sanin coin da zai tabbata da wanda zai rushe nan kusa abu ne me wahalan gaske.
Akwai coins da ake samarwa daga baya sai su gudu bayan sun samu adadin kudin da suke bukata.
Wasun kuma ba da niyan damfara a ka samar ba matsala ake samu sai kaga project ya lalace ya samu koma bayan da watakila bazai dawo ba har abada.
Wani abun duk yadda ka kai ga ilimin crypto sai ya baka mamaki, amma abu na farko da zaka fara shine neman ilimin domin zaka iya fahimtan abubuwa masu yawa wand aba kowa ne zai gane ba.
Disclaimer: bayanan dake wannan shafin ra’ayin marubucin ne sannan kuma ba financial advice bane, rubutu ne kawai wanda a ka yi shi domin ilimantarwa. kayi na ka binciken sannan ka nemi masu bada shawaran tattalin arziki kafin ka yanke hukuncin investing.