Cryptocurrency

PI NETWORK; wani ya sayi makekiyar mota da Pi guda daya

PI NETWORK; wani ya sayi makekiyar mota da Pi guda daya

PI NETWORK; wani ya sayi makekiyar mota da Pi guda daya; a yayin da ake ci gaba da hada-hadan pi a duniya an samu wani dan Indonesia wanda ya sayi wata makekiyar mota da pi kwaya daya tallintal.

pi network
pi network

An sayarwa mutumin motar a yayin da shi kuma ya bada pi network guda daya a cikin wadanda ya tara a mining da yake yi.

Babban shafin pi network na Philippines me suna pi network Philippines ne ya wallafa labarin tare da hoton mutumin da ya sayi motar, wanda ya sayar tare da motar wacce take baya dasu.

Pi network dai yana ci gaba da daukan hankulan al’umma musamman a wadannan kwanakin da a ka fara KYC wato Know Your Customer.

Ko anan Nigeria ma mun samu labarin wasu guraren da suke karban PINetwork a matsayin kudi a shaguna da guraren kasuwancin su,

Ta yaya zan sayi kaya da Pi Network di na?

Ganin cewa ka samu labarin akwai wadanda suka fara saye da sayarwa da pi network din su, tambayar yanda kai ma zaka iya sayar da naka zai iya zuwa maka a zuciya, toh ga bayanin yanda zaka sayar da pi network a nan.

Da farko kafin ka samu daman sayar da pi din ka sai kayi KYC, kafin ka samu daman yin KYC sai kamfanin Pi Network sun baka dama.

Yaya ake samun daman yin KYC na PI Network?

Yanda tsarin KYC na Pi yake shine kamafanin Pi din ne suke turawa mutane daman verification, sai dai ba lokaci daya suke turawa ba.

Idan sun baka dama kana hawa kan application na mining Pi za kaga sanarwam sai dai kawai kabi matakan da suka baka kayi verification na Pi din ka.

KARANTA: manyan masana crypto 5 daza kayi a twitter

Bayan kayi verification zaka iya sayar da Pi din ka idan ka samu me saya.

Disclaimer: bayanan dake wannan shafin ra’ayin marubucin ne sannan kuma ba financial advice bane, rubutu ne kawai wanda a ka yi shi domin ilimantarwa. kayi na ka binciken sannan ka nemi masu bada shawaran tattalin arziki kafin ka yanke hukuncin investing.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button