Easy Banking

Yanda zaka bude kuda bank account da wayar ka

Yanda zaka bude kuda bank account da wayar ka

Yanda zaka bude kuda bank account da wayar ka; Tunanin samae da Kuda ya fara ne wasu ‘yan shekaru a chan baya a yayin da wasu mutane suka hada kai suka samar da wani team domin su fara harkan banki.

Wadannan mutanen sai suka samar da wata manhaja wacce take taimakawa ‘yan Nigeria ajiye kudi da turawa wanda ake son turawa a lokacin da ake bukata, wannan manhajar itace kuda.

Wannan manhajar da ake ajiyan kudi a yanzu ta girma domin hara ta samu lasisin daman gudanar da aikace-aikacen ta daga babban bankin Nigeria wato CBN a matsayin microfinance bank, shiyasa ake kiran bankin da suna kuda microfinance bank.

Kuda bank suna saukin chaji, shiyasa za kaga mutane da yawa suna amfani dashi kuma dadin dadawa da wayar ka zaka bude ka fara amfani dashi ba tare da ka sha wahalan zirga-zirgan zuwa banki ba.

Zaka iya bude account na bankin kuda cikin ‘yan mintuna kadan da wayar ka, za kaga kudin dake shiga da fita a account din ka, da dai sauran su.

Babban dalilin samar da kuda bank shine saboda saukakawa mutanen da Nigeria daga kunci da sauran bankuna suke cusa musu.

Kuda shine suke yiwa kirari da bank of free wato ma’ana bankin kyauta a hausance, saboda idan ka bude account zasu turo maka ATM har inda kake a kyauta, zaka tura kudi ba tare da sun chaje k aba sannan zaka samu kashi 15 duk shekara idan ka ajiye kudin ka (save automatically).

Yanda kuda bank yake aiki

Kuda bank suna nan kamar sauran bankunan gargajiya (traditional bank) nesai dai su sun samar da hanyar da suke saukakawa masu amfani dasu kamar kawo ATM har garin da kake, saukin chaji da sauran su.

Kafin ka samu daman bude account na kuda bank sai ka bayar da wasu bayanan ka kamar suna, BVN, ID card, daga nan zasu bude maka account number sai ka fara amfani dashi nan take ba tare da wani bata lokaci ba.

Bayan kuda sun bude maka sabon account din ka, kuda zasu na kula maka adashi, daga nan ka zama cikakken kwastoman su.

Daga nan zaka iya karban karban ATM kuma zasu kawo maka har inda kake, sannan ko baka karbi ATM ba zaka iya amfani da application din kuda a kan wayar ka.

Da application na kuda bank zaka iya biyan bills, sayan kati da tura kudi zuwa ko ina a Nigeria.

Muhimmancin amfani da kuda bank

  1. Za kayi transfer guda 25 kyauta zuwa sauran bankuna a ko wane wata.
  2. Cikin sauki zaka blocking katin ka (ATM) idan ya bata
  3. Ba sa karban kudin kula da katin ATM (ATM mainatenance fee)
  4. Kuda bank Zasu kawo maka ATM har garin da kake a kyauta

Yanda zaka bude kuda bank account da wayar ka

Abubuwan da ake bukata domin bude kuda bank account sune kamar haka:

  • Ka kasance da babbar waya android ko ios
  • Ka tabbatar kana da email address da lamban waya
  • Shekarun kar su gaza sha takwas (18yrs)
  • Sai ka shiga nan Create kuda bank account now
  • Gurin referrel code kasa R4clXMoM

Kuda suna da tsarin bude account guda biyu wanda ake kira basic da full KYC;

Basic ya kasance ne kamar karamin account full KYC kuma babba

Abubuwan da ake bukata domin bude basic bank account na kuda;   

  • Suna
  • BVN
  • Lamban waya

Abubuwan da ake bukata domin bude full KYC account;

  • Suna
  • Lamban waya
  • BVN
  • ID card, misali katin zae, katin zama dan kasa, d.s

Dalilin da yasa full KYC account yafi basic account shine, baza ka iya transaction na kudi me yawa a basic account, full KYC kuma zaka iya transaction na kudi har miliyan daya a lokaci daya.

Adireashin kuda bank

Zai iya bukatan sanin adireshin kuda bank, wannan ne dalilin da yasa zan baiyana muku a nan ba tare da kun sha wahala ba.

Ga adireshin nan kamar haka; 151 Herbert Macaulay Way, Yaba, Lagos.

Sai dai kamar yadda na baiyana a sama, kuda bank komai online a keyi, ko da wani korafi gare ka ta email zaka tura musu kuma zasu warware maka matsalar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button