Trust Wallet; Yanda zaka fara amfani da Trust Wallet cikin sauki

Trust Wallet; Yanda zaka fara amfani da Trust Wallet cikin sauki, A wannan rubutu zaka koyi abubuwa kamar haka; menene trust wallet? Yanda ake bude trust wallet, yanda zaka sauke trust wallet a wayar ka, yanda ake tsare trust wallet.

Menene Trust Wallet?
Trust wallet, wallet ne da yake da dauke da coins masu yawa a ciki wanda binnacle ta mallaka a shekarar 2018. Trust wallet yana bada daman ajiye coins (Hold), tura coins, karban coins da saye da sayar da coins.
Kamar yadda na baiyana a sama trust wallet yana da coins masu dumbin yawa a cikin sa, daga cikin manyan coins da suke trust wallet akwai Bitcoin (BTC), Etherium (ETH), Binance coin (BNB) da sauran su.
Sannan kuma zaka iya staking coins din ka a trust wallet wadanda suke kan tsarin proof of stake kamar Tron, Cosmos da sauran su.
KARANTA: Yanda zaka tura smart chain daga binance zuwa trust wallet
Yanda zaka bude Trust Wallet
Kafin ka fara amfani da Trust Wallet sai ka sauke application din trust wallet a kan wallet a kan wayar ka, ko wane irin waya kake amfani dashi tun daga kan android har zuwa ios zaka iya zuwa playstore ko app store ka sauke application din trust wallet.
Yanda zaka sauke trust wallet a wayar ka
Zaka iya bin daya daga cikin hanyoyi biyu dake kasa ka sauke trust wallet wanda zai dace da wayar ka.
Sauke application na trust wallet a kan wayar android Download trust wallet for android
Sauke application na trust wallet a kan wayar ios Download trust wallet for ios
Bayan ka sauke trust wallet a wayar ka sai ka bude ka shiga, ka shiga create new wallet.
Sai ka rubuta recovery phrase din ka a takadda ka adana, ka tabbatar da adana shi a gurin da bazai lalace ko ya bat aba domin idan ka rasa recovery pharase na ko wane wallet to tamkar ka rasa dukiyan ka ne dake ciki.
Saboda gudun kar ya bata sai ka rubuta a gurare daban-daban ka adana idan dayan ya bata dayan baza a rasa shi ba, don haka sai ka adana shi a inda kake adana takaddan makarantan ka.
Sai ka shigar da recovery pharase din ka kamar yadda yake a jere daya bayan daya, bayan wannan shikenan ka gama bude wallet a trust wallet saura kuma ka koyi yanda za kayi amfani da trust wallet.
Yanda zaka tsare Trust Wallet din ka
Domin karawa trust wallet tsaro kana da daman kulle account din ka da kwado, domin bawa trust wallet din ka ka shiga setting sai ka duba inda a ka rubuta App Lock.
Daga nan wani sabon shafi zai baiyana yayin da za a bukaci kasa password, duk lokacin da zaka shiga trust wallet za a bukaci kasa wannan password.
Bayan ka kirkiri password sai ka taba Advance settings domin tabbatar da password da kasa a sama.
Ba wannan kadai ba hatta thumbprint zaka iya sawa trust wallet din ka, ga password, thumbprint sannan kuma an adana recovery phrase a gurin da babu wanda zai iya gani kuma ya kasance baka airdrop da wallet din da kasa kudin ka, zamu iya kiran wallet din ka suna mai cikakkiyar tsaro.
Disclaimer: bayanan dake wannan shafin ra’ayin marubucin ne sannan kuma ba financial advice bane, rubutu ne kawai wanda a ka yi shi domin ilimantarwa. kayi na ka binciken sannan ka nemi masu bada shawaran tattalin arziki kafin ka yanke hukuncin investing.