Yanda zaka tura Smart Chain daga binance zuwa trust wallet

Yanda zaka tura Smart Chain daga binance zuwa trust wallet; Binance shine mafi girman crypto exchange yanzu a duniya, sannan tana da token din ta mai suna BNB wanda ake kira native token.

Hanya mafi sauki da zaka sayi BNB shine Binance exchange, domin BNB mallakin wannan exchange ne.
To yaya kuma idan kana bukatan tura coins din ka zuwa wallet me tsaro kamar trust wallet? Da yake coins na holding an fi bukatan ajiye su a wallet na trading kuma a exchange.
Abu mafi kayatarwa shine trust wallet yana amfani da BNB smart chain ne a matsayin kudin chaji (gas fee).
Wannan ne ya kara sauwake saukin tura da adana BNB a wallet din ka na trust wallet ba tare da wata tangarda ba.
Wannan ne dalilin da yasa a wannan rubutun za muyi bayani a kan wadannan abubuwa dake kasa:
- Yanda zaka tura BNB daga Binance zuwa trust wallet
- Abubuwan da yakamata ka sani kafin tura BNB daga Binance zuwa Trust Wallet
- Binance chain da Binance smart chain
KARANTA: Yanda zaka fara amfani da trust wallet
Binance chain da Binance smart chain
Binance suna da network guda biyu na yadda ake amfani da coin din su, wato binance smart chain da binance chain.
Token ko kuma nace coin din guda daya ne, kawai yanzu Magana muke a kan network din da coin din yake, wannan ne yake bambanta abunda kake bukata ko dai ya kasance smart chain ko kuma normal BNB.
Yanda zaka tura BNB daga Binance zuwa Trust Wallet
Trust wallet daya ne daga cikin manyan wallet da muke amfani dasu wajen ajiye coins ko token din mu a yanzu a duniya.
Trust wallet ya kasance daya daga cikin DEX wato Decentralize Exchange wanda suke da tsaro fiye da exchanges na crypto.
Kar ka manta bayan ka bude trust wallet akwai recovery phrase wadanda ake bukata ka adana su domin ko da ka rasa wayan ka dasu za kayi amfani ka dawo da wallet din ka da tokens da suke ciki.
Idan ka rasa recovery phrase babu wata hanya da zaka iya dawo da wallet din ka, ka rasa ta kenan har abada, bari muci gaba da bayanin yadda ake tura BNB daga Binance zuwa Trust Wallet.
Yanda zaka tura BNB daga Binance zuwa Trust wallet
Domin karban BNB ga hanyoyin da za kabi, kar ka tura wani abu wanda ba BNB a wannan wallet;
- Bude Trust wallet
Ka bude trust wallet din ka kamar yadda ka saba a ko wane lokaci
- Ka shiga BNB
A kan screen na trust wallet za kaga coins sai ka taba kan BNB, idan ba ka ga BNB ba sai kaje gurin searching ka kunna BNB, idan ka taba zai baka daman turawa ko karba.
- Ka shiga Receive
Daga nan sai ka taba Receive. Nan take zai nuna maka address na BNB sai ka taba copy.
Wannan address din ne za sa a Binance din ka ko kuma zaka bawa wanda zai turo maka BNB daga Binance zuwa Trust wallet.
- Ka shiga Binance
Daga nan sai ka shiga Binance din ka kayi login, ka tabbatar kana da BNB a wallet din ka na binance.
- Ka shiga withdraw BNB
ka shiga kan BNB sai ka taba kan withdrawa, domin tura BNB zuwa trust wallet sai kayi paste na wallet address din BNB da dazu kayi copy a trust wallet
a gurin network sai ka zabi BEP2, kar fa kayi kuskure domin kuskure karami zai iya sawa ka rasa kudin ka ko day a kai nawa ne kuma ka rasa su kenan.
Sai ka cike sauran bayanan kuma ka duba da kyau ka tabbatar komai dai-dai kasa ba kuskure.
Yanda zaka tura Binance smart chain daga binance zuwa trust wallet
Idan kuma ya kasance Binance smart chain kake bukatan turawa saboda gas fee ko kuma shi kake sha’awan ajiyewa ga matakai da za kabi:
Ka nemi wallet din ka na smart chain a trust wallet
Abu na farko da zaka fara yi shine ka nemo smart chain, maimakon ka nemi BNB yanzu kuma smart chain zaka nema sai ka shiga kamar dai yadda mu kayi a lokacin da zamu tura BNB.
Sai ka shiga kan smart chain, ka taba receive sai kayi copy na address na smart chain.
Karanta: Menene Fundamental Analysis?
- Ka shiga withdrawa BNB a Binance
Kaje Binance sai kaje gurin assets ka shiga kan BNB.
- A gurin zaban network sai ka zabi BEP20, kayi paste na address din da kayi copy daga trust wallet.
A gurin saka address zaka sa address ne na smart chain wanda kayi copy daga trsut wallet.
Ya zama wajibi ka zabi network na BEP20 tunda smart chain kake bukatan turawa zuwa trust wallet.
Ka sani cewa zaban network din dab a dai-dai ba zai iya sawa ka rasa coin din ka ko daya kai dala malala gashin tinkiya ne.
Sannan duk lokacin da za kayi transfer na kudi ko coin ka tabbatar ka duba da kyau saboda zaka iya rasa komai idan kayi kuskure.
Da fatan ka amfana?
Turawa abokan ka na social media domin su ma su amfana.